Kyankyasu na daga cikin kwarin da suka fi addabar jama’a a gidajensu, musamman saboda yadda suke yada kwayoyin cuta ta yawunsu.

Hanyar da ta fi shahara wajen magance kyankyasu shine amfani da maganin kwari.

Ga wadanda ke son magance kyankyasu amma ba su da maganin kwari, akwai wasu ‘yan dabaru da za a iya yi domin magance kyankyasu cikin sauki kamar haka:

1. Amfani da sinadarin lausasa tufafi. Kyankyasu ba su kaunar kamshin wannan abu saboda kashe su yake. A hada sinadari da ruwa a fesa shi inda kyankyasu suke.

2. Garin koffi (Coffee). Kyankyasu na son cin wannan abu, amma idan suka ci, sinadarin ‘caffeine’ da ke cikinsa kashe su ya ke.

3. Amfani da Baking Soda da Sikari. Shima kashe su ya ke cikin sauki.

4. Amfani da garin yaji, albasa da tafarnuwa. 

Kyankyasu sun tsani warin wannan hadi, a don haka ba za su doshi inda aka barbada shi ba. 


© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top