1- قال الله تعالى: (شهر رمضان الذي أنزل فيه القرآن) الآية[سورة البقرة].
Allaah madaukakin Sarki Yana cewa: (Watan Ramãdana wanda a cikin Sa ne aka saukar da AL -QUR'ÃNI).
2- عن أبي أمامة رضي الله عنه أنه قال: يا رسول الله، مرني بأمر ينفعني الله به، قال: (عليك بالصوم فإنه لا مثل له) رواه النسائي وهو حديث ثابت.
Daga Abu-Umãmatal Bãhiliy (r.a) yace: Ya Manzon Allaah ka umurce ni da wani al'amari wanda Allaah zai amfane ni da shi, Sai Manzon Allaah(saw) Yace: (Ka lizimci azumi, saboda babu kamar shi).
3- عن سهل بن سعد رضي الله عنه أن النبي صلى الله عليه وعلى آله وسلم قال: (إن في الجنة بابا يقال له الريَّان، يدخل منه الصائمون يوم القيامة، لا يدخل منه أحد غيرهم، يقال: أين الصائمون؟ فيقومون، لا يدخل منه أحد غيرهم، فإذا دخلوا أغلق، فلم يدخل منه أحد) متفق عليه.
Daga Sahl bn Sa'ad (r.a) Lallai Annabi (saw) Yace: (A Aljannah akwai kofa da ake kira AR-RAYYÃN, masu azumi ne za su shige shi ranar Al- Qiyãmah, babu wanda zai shiga ta kofar sai su kadai. Za'a ce ina masu azumi? Sai su mi'ke, babu wadanda za su shiga ta wannan kofa sai su, idan suka shiga sai a kulle, saboda haka babu wanda zai sake shiga bayan su).
4- قال رسول الله صلى الله عليه وآله وسلم: (يا معشر الشباب! من استطاع منكم الباءة فليتزوج، فإنه أغض للبصر وأحصن للفرج، ومن لم يستطع فعليه بالصوم فإنه له وجاء) متفق عليه.
Manzon Allaah (saw) Yace: (Ya ku matasa! Wanda ya ke da hali ya yi aure, saboda shi ne ya fi kame ido (gani) da kuma kiyaye farji, wanda kuma ba shi da halin aure to ya yi azumi; domin azumi kamar dandaqa ce gare shi( ma'ana yana rage sha'awa).
5- قال رسول الله صلى الله عليه وعلى آله وسلم: (الصوم جُنَّة يَستجن بها العبد من النار) رواه أحمد وهو ثابت أيضا.
Manzon Allaah (saw) Yace: (Azumi garkuwa ne da bawa ke katange kan shi daga wuta).
6- عن أبي هريرة رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: (قال الله تعالى: كل عمل ابن آدم له إلا الصيام، فإنه لي وأنا أجزي به )، وفي رواية لمسلم: (كل عمل ابن آدم يضاعف، الحسنة بعشر أمثالها إلى سبعمائة ضعف، قال الله عز وجل: إلا الصوم، فإنه لي وأنا أجزي به، يدع شهوته وطعامه من أجلي) متفق عليه.
Daga Abū Harairah (r.a) yace: Manzon Allaah (saw) Yace: (Allaah SWT Yace: Kowane aiki na dan adam ne ban da azumi, domin azumi Nawa ne kuma NI (in ji ALLAAH) zan bada sakamakon shi), A riwayar Muslim kuwa Yace: (Ana ninka kowane aiki na dan adam, kowane lada za'a ninka shi sau goma har zuwa ninki ďari bakwai, sai Allaah Yace: sai azumi, domin shi Nawa ne kuma NI ne zanyi sakayya akansa, dan adam ya na barin sha'awar sa da abincin sa saboda NI).
7- قال رسول الله صلى الله عليه وآله وسلم: (الصيام والقرآن يشفعان للعبد يوم القيامة، يقول الصيام: أي رب منعته الطعام والشهوات بالنهار فشفعني فيه، ويقول القرآن: منعته النوم بالليل فشفعني فيه، قال: فيُشَفّعان). رواه أحمد وهو حديث ثابت.
Manzon Allaah (saw) Yace: (Azumi da Qura'ni za su ceci bawa ranar Al-Qiyãmah, azumi zai ce: Ya Ubangiji na hana shi abinci da abubuwan sha'awa da rana Ka bani ceton shi, shi kuma Qur'ani zai ce: Na hana shi bacci da dare ya Allaah ka bani ceton shi, sai Manzon Allaah Yace: Sai aba su damar ceton sa).
8- قال رسول الله صلى عليه وعلى آله وسلم: (من صام يومًا في سبيل الله باعد الله وجهه عن النار سبعين خريفا) متفق عليه.
Manzon Allaah (saw) Yace: (Duk wanda ya azumci rana ďaya sabods Allaah, Allaah Zai nisantar da fuskar shi daga wuta kimanin tsawon shekaru saba'in).
9- قال رسول الله صلى الله عليه وعلى آله وسلم: (للصائم فرحتان: فرحة عند فطره، وفرحة عند لقاء ربه، ولخلوف فم الصائم أطيب عند للله من ريح المسك) متفق عليه.
Manzon Allaah (saw) Yace: (Mai azumi ya na da farin ciki biyu: Farin ciki sanda zai yi buďa baki, da Farin ciki lokacin haďuwan sa da Ubangiji, Tabbas! Wallaahi Hamami/wari na bakin mai azumi yafi almiski kamshi da daďi a wurin Allaah).
10- قال رسول الله صلى الله عليه وآله وسلم: (فتنة الرجل في أهله، وماله، وجاره تٌكِّفرها: الصلاة، والصيام والصدقة) رواه البخاري.
Manzon Allaah (saw) Yace: (Fitinar mutum gameda iyalin sa da dukiyar sa da ma'kwabcin sa; Sallaah da Azumi da Sadaqah su na kankare su).
11- عن زيد بن خالد الجهني رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وعلى آله وسلم -: (من فطر صائمًا كان له مثل أجره غير أنه لا ينقص من أجر الصائم شيئًا) رواه الترمذي وابن ماجه وهو ثابت.
Daga Zayd bn Khalid Al-Juhaniy (r.a) Yace: (Duk wanda ya cida mai azumi Allaah zai bashi kwatankwacin ladan shi, ba tare da an rage ladan mai azumin ba).
12- عن أبي هريرة رضي الله عنه عن النبي صلى الله عليه وعلى آله وسلم قال: (ثلاثة لا تردُّ دعوتهم: الإمام العادل، والصائم حتى يفطر، ودعوة المظلوم) رواه الترمذي وابن ماجه وهو حديث ثابت أيضا.
Daga Abu Hurairah (r.a) Annabi (saw) Yace: (Mutane uku ba'a mayar da addu'ar su; Adalin shugaba, Mai azumi har zuwa lokacin buďa bakin sa, da addu'ar wanda aka zalunta).
13- قال رسول الله صلى الله عليه وآله وسلم: (من صام رمضان إيمانا واحتسابا غفر له ما تقدم من ذنبه) متفق عليه.
Manzon Allaah (saw) Yace: (Duk wanda ya azumci Ramadana ya na mai imani kuma mai neman lada wurin Allaah; Allaah Zai gafarta masa abun da ya gabata na zunubban sa).
Allaah Ya yafe ma na Ya amshi ibadojin mu.
Ďan'uwanku: Abdullahi Almadeeniy Kagarko.
© Sirrinrikemiji
Post a Comment