Fitaccen jarumin fina-finan Kannywood, Ali Nuhu ya yi ikirarin cewa wasu jaruman fina-finan na Hausa na da kudurin tsayawa takara a zaben kasar na gaba.

Jarumin ya shaidawa BBC haka ne a wata tattaunawa ta musamman da shi kuma a cewarsa a baya ma wasu a cikinsu sun tsaya takarar.

"A gaba ma yanzu, yana daga cikin irin kudurin da muke da shi, wasu daga cikinmu su fito a 2023 su tsaya takara," in ji jagoran tauraron fina-finan.

Ali Nuhu ya ce jarumai irinsu Abba El-Mustapha da Nura Hussaini duk sun taba tsayawa takara a zabukan Najeriya.

Da aka tambaye shi ko su wane ne suke da burin shiga harkokin siyasa ka'in da na'in, sai ya ce: "Ba zan iya fadar suna ba yanzu, saboda abu ne da ke kan matakin shirye-shirye".

Taurarin fina-finan Kannywood da dama ne suka mara baya ga 'yan takara daban-daban yayin babban zaben Najeriya da aka kammala a baya-bayan nan.

Lamarin da ya kai ga farraka tsakaninsu har aka rika ganin wasu na shiga shafukan sada zumunta suna yi wa juna gugar zana.

An tambaye shi cikin raha ko wata rana za a ga fasta dauke da hoton Ali Nuhu yana takarar shugaban kasa, sai ya kyalkyale da dariya yana cewa: "Ah haba! Gaba daya?"
Daga bisani ya ce "Allah dai ya tabbatar mana da alheri amma dai gaskiya muna da wadannan shirye-shirye."

An kara matsawa da tambayar ko jarumin shi da kansa yana da sha'awar tsayawa takara a zaben Najeriya? Tauraron ya ce "A gaskiya a yanzu ba ni da sha'awa".

Jaruman fina-finai da dama ne a fadin duniya ciki har da Najeriya musamman na kudancin kasar ke shiga siyasa kuma har ta kai su ga tsayawa takara.

Wani tauraron wasannin barkwanci a kasar Ukraine, Volodymyr Zelensky shi ne jarumin fim na baya-bayan nan da ya lashe zabe bayan ya tsaya takarar shugaban kasa, inda ya kayar da wani hamshakin dan siyasa kuma shugaba mai ci a kasar.

Ali Nuhu ya ce ko da yake shi ba shi da sha'awar yin siyasar takara a yanzu, amma a shirye yake ya mara baya ga duk wani tauraron fim da zai tsaya takara.

Rarrabuwar kan da ke tsakaninsu sakamakon tallata wasu 'yan siyasa wadanda ba 'yan Kannywood ba, ba zai faru ba idan su da kansu ne suka fito takarar, a cewarsa.

"Ina tabbatar miki da cewa 'yan fim suna da hadin kan da ba a taba tunani ba, sabanin da ake gani tsakaninsu a shafukan sada zumunta, lamari ne da ke faruwa kamar a kowanne fagen sana'a," in ji Ali Nuhu.

An tambaye shi ko idan lokacin da ya yi sha'awar tsayawa takara, shin zai iya janye wa Adam Zango idan takara ta hada su kan wata kujera daya? Ali Nuhu ya ce: "Kwarai kuwa".

BBChausa.

Post a Comment

 
Top