π± Tana matukar kaunar mijinta sosai har ta kai ba ta ma son kawayenta da ma mutan dake unguwa suyi magana da shi. Tana Kuri da shi, tana bugun gaba da shi a duk inda tashiga tana nuna ai ita Matar wane ce, sbd mijinta irin Wanda duk wata macen kirki take nema ne ace shine uban yayanta kuma mijinta Har abadan.
π± Wata rana sai yayi wata iriyar kwalliya mai kayatarwa, ya cancara ado sosai tayadda yatafi da tunaninta kuma duk wacce ta ganshi a lokacin sai ta yabashi, (Masha Allah, Tabarakallah). Sai ta dauke shi Hoto ta ajiye a kan wayarta.
π± Wata rana sai tayi tunanin bari ta burge kawayenta, kuma tayi musu kwalelen basu samu miji irin nata ba, sai ta dora hoton sa akan DP (gurbin fuskarta a kafar sadarwa) akan Facebook da WhatsApp.
π± Wata kawarta (wacce basu taba ganin juna ba, sai dai a social media) tana ganin shi kuwa sai duk tabi ta rikice, taji duk Duniya babu wanda takeson Aure kamarsa, tayi ISTIKHARA (taba Allah zabin abunda yafi Alkhairi), sai Kai tsaye ta shiga binciken inda yake, sbd Zuciyarta tana da kyakkyawar niyya da buri akanshi. Sai kuwa Allah yabata nasarar samun shi, cikin yen lokaci kalilan ta karkato akalar zuciyar shi izuwa gareta, sbd Allah ya bata zalaqa, fasaha, kwarkwasa, yauki, salo da kuma hikimar zance fiye da matarsa, kuma ta fi Matarsa kyau nesa ba kusa ba.
π± Manya suka shigo lamarin yaje yaganta kuma yaji ta yimasa, itama haka, lamari yayi nisa sai yasanar da Uwargida cewa: zai kara Aure abisa yadda Addini yabashi dama da wata yer Social media, kuma ya je wajanta sun ga juna, an kammala komai.
π± Akayi Aure kamar yadda Shari'a tayi tanadi, uwar gida hankalinta yakasa kwanciya a lokacin da taga ai kawarta ce ta facebook mijinta ya auro, tayi nadamar sanya hotonsa a Social media, ciwon Zuciya yakamata, takasa tabuka komai acikin gidan, har yakai jininta yahau sosai sbd tunani. Ahakanann kuma ciwon barin jiki yakamata. Ta samu tawayar lafiya.
π± To nidai *Rismawy* banga wani abin tashin hankali ba anan, auren kawa ba wani abin cin amana bane kuma ba haramun bane a shari'ar Allah, gwara ma kin hakura kin rungumi qaddara6, sbd larabawa suna cewa *Idan abinda ba makawar zuwansa yazo, kawai a yi maraba da shi*.
SAI AKIYAYE...
A wajan tayiwa wasu kwalele, ashe akwai rabon kawarta acikin gidanta, kuma ta aure mijinta. ta siyar da mijinta ga wata. Idan har ba kyaso wata ta shigo to ki alkinta mijinki, amma hakan bazai taba hana Allah yatabbatar da abinda yakeso.
GANI GA WANE... YA ISA WANE TSORON ALLAH.
Allah yasa mudace kuma ya azurtamu da zuriya tayyibah.
✍π» *Idris M Rismawy*
© Sirrinrikemiji
Post a Comment