‘Yan uwa mata ku sani samari mayaudara sun fi samari na kirki shiga rai, sun fi su iya nuna so da kauna a gare ki. Su kan kwantar da kai a gare ki komai wulakanci, ga su da azababban na ci tun kina kin kula su har sai sun jawo hankalinki. Hakan ta sa gane saurayi mayaudari abu ne mai wuya, domin abu ne da ke zuciya sai dai in kin bi wasu matakai da kuma dubaru kafin ki gane wasu siffofin.

Dabarun da samari mayaudara suke bi dan yaudarar ‘yan mata suna da yawa, amma ga kadan daga cikin su.

– Da farko, su kan yi farautar budurwar da suke so su yaudara imma dan kyanta, ko halittarta ko kimarta kowani dalili na su ko dan fasikanci.

– Su kan yi nazari a kan halayenta kamar akidarta me tafi so wato idan ita ustaziya ce, su kan yi shigar ustazai su zo wurinta, in sun ga dama su kan ruko littafi na ustazai kamar salasa usulu, kitabul tauhid da dai sauran su, sai su zo wurin mace domin a biyo mata ta hannar da ta fi saboda tsabar yauddara.

-Idan ke sayyada ce, su kan yi miki shigar sayyadi su zo miki hira, in sun ga dama sai su ruko diwani ko wani dan littafin na kasida, idan ke me yawan karatun soyayya ce, sai su zo miki da littafan soyayya sabon shigowa ko ci gaban wani littafi shahararre, yana rike a hanunsu.

-Idan ke ma abociyar son holewa ce, haka zai yi miki shiga ta ‘yan holewa.

-Idan ke abar tausayi ce, zai zo da sunan zai taimake ki har makaranta ma zai saki.

-Zai tunga bin ra’ayinki ta yanda bai son saba miki, ga su da dadin baki, su kan yi miki kuka ko su durkusa miki kasa suna baki hakuri su kan fada miki kalaman kwantar da hankali da rantsuwa wadda saurayi na kirki ba zai iya fada miki ba.

Wannan siffofin na sama, siffa ce ta samari ma yaudara, amma sun fi yin amfani da su wajen kananan ‘yan mata kamar yan shekara 18 zuwa kasa. Sakamako ‘yan mata a wannan lokacin suna da nakasu sosai a tunani, a wannan lokacin soyayya kawai suka sani su kan bujire wa kowa a kan soyayya ko da iyayensu ne.

Idan samari za su yaudari manyan ‘yan mata, su kan yaudare su ne da kudi ko abubuwan duniya sakamakon a wannan lokacin su manyan mata da ke shekara 20 zuwa sama su matsalar su mota, kudi masu yawa da sauran su.

Abubuwan rayuwa kamar a ara wa mata mota, yi mata karyar za a saya mata mota ko wasu abubuwan har sai ta saki jiki sannan a yaudare ta a gudu.

Wasu mayaudaran samari su kan kai kayan tambaya, ko ma kudin aure ko su tura iyayensu domin a yi musu tambatar aure, amma daga nan ba sa sake aiko komai sai su yi ta soyayya da budurwa har sai sun yaudare ta.
Wasu ma yaudaran samarin su kan yaudare ki da hadin bakin abokansa ta hanyar shirya miki makirci. Kamar sa miki kwaya a lemo da sauran su.

Akwai dalilai masu yawa da ya sa samari suke yin yaudara, amma ga kadan daga cikin su.

-Daukar fansa, wato idan wata mace ta yaudare su, sai su kasa yin hakuri sai su je su yaudari wata.

-Rashin tsoran Allah na hakika.

– Son su yi fasikanci da budurwa.

-Samun budurwar da za a tunga zuwa fati da sauran guraren holewa da ita.

Yadda mace za ta maganin samari mayaudari.

-Ka da ki taba zurfafa son saurayi kowaye shi kuma ko me yakawo gidan ku.

-Ki zama mai yawaita addu’a da neman kariya daga sharrin samari mayaudara.

– Ka da ki kuskura ki yi yaudara ko da kadan ne.
-Idan saurayi ya zo kafin ki amshi soyayyarsa, ki ba shi akalla kwana biyu ko kuma sati daya, kafin nan ki je ki yi istihara a kan sa, in sha Allah in bana gari ba ne ba zai dawo ba domin Allah zai wargatsa nufinsa a kanki.

-Ki yawaita shigo da iyayenki da nasa cikin al’amuranku na soyayya.

-Ka da dan ya kawo miki kudin aure ki saki jiki da shi.
– Da zarar kin ga canji a tare da shi, ki yi kokari wajan samun mafita ta hanyar binciken sa ko na kusa da shi. 

A cikin minti goma zai iya zuba miki dafin da zai shafe tarihin rayuwarki, ya to zarta ki da danginki duka, ya kaskantar da ke, ya bata tarihin zuriyarki shi kuma ya kama gabansa. Dan haka, ‘yar uwa da kin fuskanci saurayi mayaudari ne, to ki yi kokarin raba gari da shi ta hanyar kar ya sake zuwa unguwarku.

Samari mayaudara abokan juna ne su kan taimaka wa junansu wajen gudanar da wannan mummuunar akida nasu. Su kan yi musanyen unguwa dan wannan unguwar ya bai wa dan wancan unguwar sirrin unguwar.
Kashi saba’in da biyar cikin dari na samari mayaudara suna yi ne dan su yi lalata da ke.

Daga karshe ina jan hankalin ‘yan mata da su kula da samari mayaudara daga fada wa tarkunsu. Tabbas abu wata mace da da namiji da ba zai iya yaudara ba, amma dan kika tsare kanki, sannan kuma kika ci gaba da addu’ar neman tsari daga wajen Allah, to lallai za ki kubuta daga sharrin wadanan samari masu muyagun akida.

Allah ka shirya irin wannan samari masu yaudara, sannan ka tsare ‘yan mata daga fadawa tarkunsu.


© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top