azumi a wannan tafiya.
Idan matafiyi ya yi azumi, azuminsa ya yi, saboda hadisin Anas xan Malik – Allah ya yarda da shi – ya ce, “Mun kasance muna tafiya tare da Manzon Allah ( ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ). Mai azumi a cikinmu bai aibata wanda ba ya azumi, hakanan wanda ba ya azumi bai aibata wanda yake azumi” [Bukhari ne ya rawaito shi].
Sai dai da sharaxin kada azumin ya yi masa wahala, idan ya yi masa wahala, ko kuma ya cutu da shi, to ya ajiye azumin shi ya fi.
Saboda Annabi ( ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ) ya ga wani mutum a tafiya yana azumi, an masa rumfa saboda tsananin zafin rana, mutane sun kewaye shi, sai Manzon Allah ( ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ) ya ce, “Ba ya cikin aikin alheri yin azumi a halin tafiya” [Bukhari ne ya rawaito shi].
3 - Ciki Da Shayarwa
Mai ciki ko mai shayarwa idan suka ji tsoron cutuwa idan suka yi azumi, to sai su sha azumin, su rama kamar yadda marar lafiya yake ramawa, saboda faxin Manzon Allah ( ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ) “Haqiqa Allah Maxaukakin Sarki ya sauke wa matafiyi azumi, da rabin sallah, haka ma an sauke wa mai ciki da mai shayarwa azumi” [Tirmizi ne ya rawaito shi].
Idan kuwa mai shayarwa ta ji tsoron cutuwar xanta, sai ta sha ta rama, ta kuma ciyar da miskini a kullum, saboda faxin Abdullahi xan Abbas – Allah ya yarda da shi – “Mai shayarwa da mai ciki idan suka ji tsoron cutuwar ‘ya’yansu, su sha azumi, su ciyar” [Abu Dawud ne ya rawaito shi].
4 – Haila Da Jinin Biqi
Wajibi ne macen da jinin haila ko biqi ya zo mata ta ajiye azumi, haramun ne a kanta ta yi azumin, in kuma ta yi bai inganta ba, sai ta rama, saboda abin da ya tabbata daga Aisha – Allah ya yarda da ita – an tambaye ta dangane da rama azumi da mai haila take yi,
amma ba ta rama sallah, sai Nana Aishatu ta ce, “Hakan yana samun mu, sai a umarce mu da rama azumi, amma ba a umartarmu da rama sallah” [Bukhari da Muslim suka rawaito shi].
© Sirrinrikemiji
Post a Comment