Babban sakataren Hukumar Taca finafinai ta jihar Kano, Isma’il Na’abba Afakallahu, ya bayyana cewa, babban burinsa shi ne ya kai masana’antar shirin fim ta Kannywood matakin da za ta iya gogayya da takwarorinta na kasashen duniya.

Shugaban hukumar tace-fina-finan da dab’i ya ambata wannan ne a ranar 18 ga watan afrilu 2019 a ofishinsa bayan kammala kaddamar da kwamitocin bayar da tallafi ga halattattun ‘yan masana’antar. Afakalla ya nuna matukar kishinsa ga masana’antar yadda yake bin duk hanyar da ya ga ta dace don tallafar masana’antar. A irin namijin kokarnsa ne har wannan tallafin ya tabbata.

Ya ci gaba da cewa gwamnatin jihar Kano tana sane da irin matsalolin da masana’antar ke ciki kuma ta damu don ganin ta kawo karshen duk matsalolin wanda makasudin wannan taro yana ciki wato samar da kwamitin da zai bayar da rance ga masu shirya fim da duk wani abu da ya dangance shi da mawaka da marubuta. A hangenmu muna ganin kalubalen sana’ar akwai rashin kudi akwai rashin ilimi akwai rashin tsari irin na kasuwanci na zamani sannan ma akwai rashin wadatattun kayan aiki na zamani da tafiyar da su. Wadannan kalubale ne gare mu ba yanda za a yi mu zauna mu zuba wa tulin wadannan matsaloli ido a matsayinmu na jagorori sana’armu ta sami tangarda. Kuma akasarin masu wannan sana’armu matasa ne a cikin sana’ar suke ci suke sha suke ma rufawa kansu asiri da ma wani nasu. Wannan ya sa gwamnatin jihar Kano ta Maigirma Dakta Abdullahi Ganduje mai kishin al’ummarta ta ta amince da ta zama garanto don a bayar da tallafin nan don ta taimaki al’ummarta su yi dogaro da kansu.

Kudin Kyauta ne ko Bashi Kuma wa Za a Ba wa?
Wannan kudi ba kudi ne da za a bayar kyauta ba. Kudi ne da za a bayar bashi domin ta yarda za a bunkasa sana’ar. Wannan kudi kofa a bude take ga kowa, kowa ya cancanta ya karba in har dan halalin masana’antar ne kuma ya cike duk ka’idar da kwamiti da hukumar tace fna-finai da dab’I ta ambata sai wanda ba ya so.
Wanne irin Sharudda Hukumar ta Shimfida Don Karbar Wannan Kudin?
Dalilin fitar da wadannan kwamitoci har guda biyar an fitar da su ne don tabbar...

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top