Gwamnatin Najeriya ta bayyana fargabar cewa, kasar ba za ta iya magance matsala ko kalubalen rashin ayyukan yi a tsakanin al’ummarta nan kusa ba.

Gwamnatin ta sanar da haka ne ta hannun ministan Kwadagonta da samar da ayyukan yi Chris Ngige, wanda yayi hasashen cewa adadin marasa aikin yi a kasar zai karu daga kashi 23.1 zuwa kashi 33.5 a shekara mai kamawa.

Ngige ya bayyana hasashen ne yayin gabatar da jawabi a wani taron kwanaki biyu a Abuja, kan nazarin magnace matsalar rashin aikin yi a Najeriya.

Cikin rahotonta na shekarar 2019, hukumar kididdiga ta Najeriya ta ce kashi 23.1 na ‘yan kasar basu da aikin yi, yayinda kashi 16.6 suke aikin da bai wadace su ba.

Wannan rahoto kan rashin ayyukan yi da ke nuna tilas gwamnatin Najeriya da sauran masu ruwa da tsaki su tashi tsaye don magance wannan kalubalen, ya zo ne a dai dai lokacin da kasar ke fuskantar matsalolin sha da cinikin miyagun kwayoyi tsakanin matasa, sata da yin garkuwa da mutane, tsageranci a yankin Niger Delta mai arzikin man fetur da kuma sauran manyan laifuka da ke ciwa al’ummar kasar tuwo a kwarya.

RFIhausa.

Post a Comment

 
Top