Wata kotu a garin Dar-es-Salam, kasar Tanzania, ta amshi karar da wani dan sanda mai suna Darius Makambako ya shigar a kan ya dauki hayar makwabcinsa domin ya yi wa matarsa ciki amma ya gaza yi mata.

Darius Makambako, dan shekara 50, da matarsa Precious, 'yar shekara 45, sun sami kansu a cikin tsananin bukatar haihuwa. Shekararsu shida da aure amma ba su sami ko da bari ba. Hakan ya sa suka tuntubi likitansu, shi kuma ya tabbatar masu da cewar Darius ba ya haihuwa.

Ganin hakan ya sanya Darius ya dauko hayar makwabcinsa mai suna Evans Mastaro, dan shekara 52, shi ma ma'aikacin dan sanda, domin ya yi wa matarsa ciki.

A ganinsu, tunda Evans yana da aure, har ma ya haifi kyawawan 'ya'ya mata guda biyu wadanda ma suke matukar kama da shi Darius din, shirin nasu zai tafi daidai yadda ake so.

Darius ya biya Evans Shilling 2,000,000 na kudin kasar (daidai da Naira 10,000) a matsayin kudin aiki. Sannan ya ba shi yini uku a cikin sati, na tsawon watanni goma a cikin shekarar 2016 a matsayin kwanakin aiki.

Evans ya kama aiki ba wasa, sai da ya yi sau 77 amma Precious ta gaza daukar ciki.

Rahotanni sun ce Precious, malamar jinya a wani asibitin kudi, ta dauki hutun watanni uku a gurin aikinta (daga watan Maris zuwa Yuni, 2016) domin ta sadaukar da lokacin gurin kwanciya da aminin mijinta, kuma makwabci, domin ta sami damar haihuwar danta na farko. Sai dai mutumin ya gaza yi mata cikin duk da a lokuta da dama mijinta na bari su kwana, su yini a bisa gado.

Da Darius ya ga amininsa Evans ya gaza yi wa matarsa Precious ciki a tsawon watanni goma sai ya tursasa shi a kan ya je asibiti domin a duba shi. Dole Evans ya je asibitin a watan Junairu, 2017.

Sai dai kowa ya girgiza da ya ji cewar bincike ya bayyana cewa Evans Mastaro, mahaifin 'ya'ya biyu mata masu kama da Darius, ba ya haihuwa. Hakan ya sa aka tursasa matarsa, inda ta bayyana cewa ba shi ne mahaifin yaran ba; dan uwansa Edward ne mahaifin yaran na gaskiya.

"An tursasa ni kwanciya a cikin sirri da dan uwansa inda muka haifi yaran nan guda biyu, bayan na ga mijina ya gaza yi min ciki a cikin shekaru biyun aurenmu," Angela ta fada.

A yanzu Darius ya maka Evans a kotu a kan ya maido masa da kudinsa tun da ya gaza cika yarjejeniyar da suka yi.
Sarauniya.

Post a Comment

 
Top