Jarumar fina-finan Hausa, Amina Amal ta bayyana yanda dambarwarta da Hadiza Gabon ta kasance akan zargin Madigo da kuma bidiyon cin zarafi daya watsu a shafukan sada zumunta.

A hirar da ta yi da jaridar Daily Trust,Amal ta bayyana cewa, da farko dai wasu hotunane ta saka a shafinta na sada zumunta inda hotunan suka jawo cece-kuce sosai, daga baya sai ta saka wani sakon sirri da bai yiwa Hadizar dadi ba.

Tace bayan nanne sai wani me bayar da umarni ya kirata yace zasu yi magana, tana gida sai ya sake kiranta, tana fitowa sai taga wata mota, sai ga Hadiza Gabon ta fito daga ciki, ta kamata da duka, suka shiga cikin gida ta kwace mata waya ta goge sakonninta dadai sauran wasu abubuwan dake wayarta.

Da aka tambayeta me zata ce akan abinda aka ji tana cewa sharrin kwayane ya sata hakan.

Sai tace duk abinda aka gani a bidiyonnan da gaskene, Hadizar ta tafi da wayarta, dan haka sai ta bita shagonta dan ta karbo wayar, tace can ma da taje sai Hadizar da wasu mukarrabanta ciki hadda direbanta suka kamata da duka, kuma duk abinda ta fada a bidiyon ta fadane dan kawai ta samu ta bar gurin saboda tana cikin tashin hankali.

Ta kara da cewa, yanzu dai ta zauna da wasu lauyoyi da suka sha alwashin taimaka mata wajan dawo da martabarta, sannan tana da matsalar zuciya, wannan abin da ya faru da ita ya jawo mata rashin lafiya dan haka sai da taga likita amma yanzu da sauki.

Ta kara da cewa, har yanzu tana girmama Hadiza Gabon dan tana gaba da ita, kawaidai tana son dawo da martabarta da ke neman zubewane shiyasa ta nufi kotu.

Post a Comment

 
Top