Yadda mai ciki za ta gane namiji ne a cikinta ko macece ce, tun kafin aje wajen likita.

Sanin kowa ne cewa yanzu Allah ya hore wasu hanyoyi da ake gane shin namiji ne a cikin mace ko mace ce?!, tun kafin a haife.

To ga wasu hanyoyi da za ki gane abinda ke cikin ki ba tare da likita

Idan ki ka ji wadannan alamomi to namiji ne a cikin ki, in kuma ki ka
ji kishiyar su to mace ce.

1- Idan jikin ki ya fiye kyau mai kayatar wa, to namiji ne acikinki.

2- ldan 6angaren dama na cikin ki ya fi nauyi, namiji ne.

3- rashin motsin ciki sosai, shi ma alamar namiji ne.

4-ldan kan nonon ya yi jajur, alamar dan cikin namiji ne.

5- yawan kasala lokacin goyon ciki, alamar namji ne.

6-idan mai ciki ta na fara daga kafar dama in za ta yi tafiya to da alama namiji ne a cikinta.

7- idan nonon 6angaren dama ya fi
girma to namiji ne a cikin.

8- idan kan nonon dama ya fi girma, shi ma haka.

9- idan ki ka ga cikin ki ya kewaye, alamar da namiji ce.

10- ldan ki ka tatsi nonon ki ki ka gan shi mai kauri sosai, to alamar kin dau namiji.

11- idan idon mai ciki ya yi ruwan dorawa, alamar jariri namiji ne.

12- mace ta dinga wasu dabi‘u wanda da ba ta yi.

Duk wadannan alamomi su na nuna cewa ‘Dan cikin namiji ne.

Idan kuma ki na jin sa6anin su to mace ce.




© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top