A yayin da mutane ke fama da zafi a wannan lokaci da yanayi, haka zalika wasu dabbobi da kwari kamar su macizai, kunamu, ke fama da shi, hakan yasa suke fitowa domin samun ni’ima.

Wasu masana kiwon lafiya sun bayyana cewa a wannan lokaci na zafi mutane sun fi kamuwa da cutuka kamar Sankarau, Zazzabin cizon sauro, Saran maciji, kunama da sauran su.


Ga wasu hanyoyi 10 da za a kiyaye domin gujewa fadawa cikin ire-iren matsalolin a lokacin zafi:

1. A daina barin tagogi da kofofi a bude ba tare da a na kula da duk wani motsi ba. Za a iya saka murfin kofa mai raga, kafin ainihin kofar shiga saboda kiyaye wa.

2. A tabbatar an duba rassan itatuwa da kuma tarin ganye dake karkashin itatuwa domin gujewa cin karo da macizai.

3. A tabbatar ana tsaftace muhalli ana rufe kayan abince don guje wa kamuwa da cutatuka.

4. A yi amfani da maganin sauro domin gujewa kamuwa da Zazzabi.

5. A yawaita shan ruwa.

6. A kula da tsaftace yara.

7. A nome duk ciyayi dake cikin gida da wajen gida domin hana macizai,tsaka,kulba,kunama da sauran kwari samun mazauni.

8. Za a iya amfani da maganin kawar da macizai da kwari ko da na gargajiya ne da na zamani domin hana macizai shigowa gida.

9. Kada a yi gangancin kashe maciji domin wasu macizan ka iya zama ajalin mutum idan ba kwararre ba ne.

10. A guji cin abinci kamar su wake, madara, kifi da sauran su idan dare ya yi sosai domin guje wa matsalar ciwon ciki.




© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top