Wata mata mai suna Hilda Lainjo daga ƙasar Amuruka ta yi tattaki na musamman zuwa Nijeriya domin ta ziyarci Maulanmu Sheikh Dahiru Usman Bauchi. Lainjo ta shaidawa Shehu RTA cewa ita daga Amuruka take kuma tace dalilin zuwanta shine domin ta ga Shehu ta ziyarce shi.

Ga dai abinda ta shaidawa Shehi da bakinta:

" Ya shehi ni dai daga ƙasar America nake nazo nan najeriya ne domin inganka inga lafiyarka in ziyarceka kayi min addu'a insamu albarkanka da kuma kwanciyar zuciyata a cikin rayuwata ya sheikh."

Shehi yayi maraba da zuwanta daga bisani kuma yayi mata addu'a kamar haka :

" To Allah ya biya miki dukkan bukatun ki na duniya da na lahira. Ameen thumma amin."

Allah ya ƙarawa Shehu girma da karama amin.
Rariya.

Post a Comment

 
Top