Hadin da ake yi wa fuska na nan
da dama. Ya kamata zuwa yanzu
masu karatu su gane wane irin
hadi da nake nufi. Amma idan akwai
wadanda ba su san wannan hadi
ba, zan yi musu bayani. A takaice
dai hadin fuska, shi ne, irin-kwabe-
kwaben da ake yi a shafa a fuska
domin magance wasu cututtukar
da ke damun fatar jiki ko ta fuska.


Wannan hadin na cire kwayoyin
cutar da ke cikin fata da gyara shi
da kuma kara karfafa karfin fata.

Ba tare da an kashe kudi a
kantuna sayen maganin gyaran
fata ba, akwai yadda za a iya hada
wannan hadi ta hanyar amfani da
kayan girki kamar haka:

• Za a iya hadin ruwan lemun
tsami da na zuma sannan a shafa
a fuska ko jiki, domin inganta
hasken fata da karfafa fatar jiki da
kuma hana fesowar kuraje.

• Akwai hadin ayaba da kwaiduwar
cikin kwai da man zaitun. Idan aka
yi wannan hadin, sai a shafa a
fuska na tsawon minti ashirin
sannan a wanke, shi ma wannan
hadin domin gyaran fatar jiki da
kuma na fuska ne.

• Hadin ruwan lemun zaki da
ruwan kwai da kuma kurkum na da
matukar muhimmanci sosai domin
yana taimakawa wajen gyaran fata,
musamman ma ga amare.

• Garin bawon lemu wanda sai an
busar sannan a daka a tankade
sannan a hada da ‘baking soda’
shi ma yana magance cututtukan
fata sosai.

• Akwai hadin ruwan kwakwa da
garin bawon lemun zaki da kuma
madara. Wannan irin hadin na
sanya fata sulbi sosai.

• Hadin fiya da man zaitun da
madara na da muhimmanci sosai
ga inganta fata domin na magance
gautsin fata da kuma sanya fata
taushi.

• Ayaba da ruwan lemun zaki da
kuma kindirmo idan aka kwaba su
ana shafawa a jiki na magance
tattarewar fata.




© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top