Kotu ta hukunta wasu masoya a kasar Kenya bayan da ta kamasu da laifin damun jama'a da ihu lokacin da suke jima'i. Jama'a ne suka kaiwa 'yansanda korafin Chacha Mwita dan shekaru 24 da masoyiyarshi Cynthia Mauhokha me shekaru 31 yayin da suke daki suna abin.

Har lokacin da 'yansandan suka karaso wurin basu gama ba, suma sunji ihun nasu, nan suka shiga dakin suka kamasu.

An gurfanar dasu a gaban kotu kuma sun amsa laifukansu. Daga nanne sai kotu ta bayar da belinsu bayan da suka biya kudin diyya.

Post a Comment

 
Top