Tsohon na hannun damar shugaban kasa, Muhammadu Buhari kuma jigo a jam'iyyar PDP, Injiya Buba Galaduma ya bayyana cewa Duniya ta shaida Atikune ya ci zaben shugaban kasa amma Buhari yayi murdiya ya kwace.

Buba Galadima yace APC magudi da tayi inda jami'an 'yansanda dana soji da hukumar abe suka taimaka mata, yace cewar da ake hukumar zabe me zaman kanta a bakine kawai a zahiri ba zaman kanta take ba.

Yace yana kalubalantar shugaba Buhari da duk 'yan APC su fito su rantse da Qur'ani, kiristoci kuma su rantse da baibul cewa ba magudi suka yi suka ci zabe ba.

Galadima ya kara da cewq magudin zaben da Buhari yayi ya nuna cewa yaki da rashawa da yake yi ba da gaske bane dan ba satar kudin gwamnati bane kadai rashawa ba, tana farawa ne daga ingancin zabe

Post a Comment

 
Top