Kamal S. Alkali daya ne daga cikin manyan daraktoci da kuma masu tsara labarin fim a masana’antar shirya fina-finan Hausa da aka fi sani da Kannywood, shi ne Babban Daraktan Gudanarwa na kamfanin shirya fina-finai na Kamal Films International da ke Kano. A tattataunarwar da ya yi da Aminiya, Daraktan wanda ya lashe Gwarzon Darakta yayin gasar City People Entertainment Awards a shekarar 2017 ya bayyana dalilin da ya sa ’yan fim suka shiga siyasa gadan-gadan da abin da ya kamata Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa Kannywood kafin ta ruguje. Ga yadda hirar ta kasance:
Aminiya: A bana yawan fina-finan da ake fitarwa ya ragu, inda kuma hankalin ’yan fim ya raja’a wajen yi wa ’yan siyasa kamfe, a ganinka me ya jawo haka?
Kamal S. Alkali: A zahirin gaskiya Kannywood ta samu kanta cikin ukuba tun a shekarar 2017, kuma har zuwa yau ’yan fim kuru kawai suke wajen shirya fim ba tare da riba ba, na san cewa mun zauna a lokuta daban-daban don tattauna yadda za a shawo kan matsalar kasuwanci da rarraba fina-finai, amma abin ya ci tura. A yanzu da nake magana da kai da yawa daga cikin ’yan fim ba su da jarin da za su shirya fim ma, don haka da zaben bana ya gabato sai ’yan fim suka ga wata hanya ta samun kudin ta samu, sai kawai suka rungumi yi wa ’yan siyasa kamfe. ’Yan fim sun yi amfani da farin jininsu wajen tallata ’yan siyasa, inda hakan ya zame musu wata hanya ta samun kudin shiga.
Ta yaya Kannywood ta samu kanta cikin wannan mawuyacin hali?
Kowa ya sani Kannywood ta dogara da sayar da fina-finai a faifan CD da DBD ne, don haka da fasaha ta karu inda za ka iya kwafar fim ka sa a wayarka ko na’urar flash kuma ka tura wa miliyoyin mutane, sai aka daina sayen fim.Mutum daya zai saya sannan ya tura wa mutane da yawa, hakan ya rage mana yawan fina-finan da muke fitarwa, sannan an bar mu da yaki da masu satar fasaha, inda hukumomin da suka kamata su taimaka suka nade hannunsu, ba tare da yin komai a kai ba.
Daga nan sai muka koma cin kasuwa da tasoshin talabijin, sai mu sayar da fim mu ci riba kadan, a farko tasoshi uku ne, daga baya biyu suka daina sayen fina-finai, kuma ka san ’yan fim suna da yawa, hakan ya sa fina-finan da ake fitarwa suka fi karfin wannan tashar da ta rage da ke sayen fim, inda ta koma zabe, hakan ma ba daga an sayi fim dinka za a ba ka kudinka ba, hakan ya sa ’yan fim da yawa karyewa.
Ga shi Arewa ba kamar Kudu ba, wato babu silimomi na zamani da za a rika nuna fim, don haka da siyasa ta zo sai duk ’yan fim suka koma kamfe don mu samu damar ci gaba da ciyar da iyalinmu ko daukar nauyin kanmu.
Me za ka ce a kan jita-jitar da ake yadawa cewa ’yan fim sun yi wa ’yan siyasa kamfe ne ba tare da sun gabatar musu da matsalolin da Kannywood ke fuskanta ba?
A gaskiya daga farko kowa abin da zai samu daga wurin ’yan siyasa ne damuwarsa, amma daga baya sai muka yi karatun ta-natsu, muka fada wa kanmu cewa shin mene ne matsayinmu bayan mun kammala kamfe dan takara ya ci zabe? Sun ba mu kudi mun yi musu kamfe, wadansu ma za su yi tunanin sun riga sun biya mu kudi mun yi musu kamfe, hakan ya sanya muka fara ba su bukatun Kannywood a rubuce. Kuma da yawansu sun ce za su yi aiki a kai idan sun samu nasara a zaben.
Kamar wadanne bukatu kuka nema a wurin ’yan siyasar?
A zahirin gaskiya za mu iya cewa babbar matsalar Kannwood ita ce rashin kasuwaci da dillanci da kuma rarraba fina-finanmu, kuma har zuwa yanzu babu wata hanya mai bullewa da aka samo da za ta kai mu ga gaci. Muna so gwamnati ta farfado mana da hanyoyin kasuwancinmu, sannan a matakin Gwamnatin Tarayya muna so gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta gina mana silimomi na zamani a jihohin Arewa 19. Muna so gwamnatin Buhari ta ba mu rance mai sauki kasancewar a yanzu da nake magana da kai ma da yawa a cikin ’yan fim ba su da jari. Muna so gwamnati ta fahimta cewa ta hanyar gina silimomi ma za ta rika samun kudin shiga, ba mu ce gwamnati ta ba mu kudi kyauta ba, domin za mu biya bashin da aka ba mu.
Muna so Buhari ya ba hukumomin da ke yaki da satar fasaha umarnin su tashi tsaye wajen kawar da masu satar fasaha, saboda idan ba haka ba, to Kannywood ta kusa rugujewa.
Muna so gwamnatin Buhari ta dauki matakin gaggawa a kan masu satar fasaha domin Kannywood wata masana’anta ce da miliyoyin mutane suke ci a karkashinta, kuma tana kunshe da dubban matasa, don haka idan masana’antar ta durkushe to za a kara samun matsalar tsaro da ta hada da sacewa da garkuwa da mutane, sace-sace da fashi da makami da sauransu.
Sannan muna so manyan mutane da suka yi shahara su rika tallata fina-finan Kannywood, bari in ba da misali a Indiya akwai wani fim mai suna ‘Bahubali’, tun kafin fim din ya fita kasuwa Firayi Ministan kasar Indiya, Narendra Modi ya kalli fim din, sai ya je shafin sadarwa na Twitter ya rubuta yaya zai kashe babban jarumin shirin fim din? Hakan ya sa mutane suka ce tunda har Firayi Minista ya yi magana a kan fim din, to, babban fim ne, kuma maganarsa ta sanya mutane da yawa suka kalli fim din.
Akwai wani lokaci ma da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar ya kalli wani fim din Amurka inda ya yi magana a kansa, hakan ya sa aka kalli fim din sosai a Najeriya. Don haka idan manyan mutane da suka shahara za su rika magana a kan fina-finan da muka yi, to hakan zai taimaka wajen bunkasa masana’antarmu.
Duk da matsalar kasuwanci da dillanci fina-finai da Kannywood ke fuskanta, shin kana da wani shiri na ci gaba da shirya fina-finani?
Eh, haka ne, ina da labarai masu yawa da aka rubuta da Hausa, zan juya su in mayar da su na Ingilishi, saboda ba za mu dogara da silima daya da ke Kano ba kawai, yaya masu son kallon fim za su kalli fim a wasu jihohi? Babbar hanyar da zan ci gaba da shirya fina-finai kuwa ita ce in koma daukar fina-finaina da Ingilishi, inda za a rika haska su a dukkan silimomin kasar nan har da ma na duniya.
Yanzu wani abu masu kallo za su saurara daga gare ka?
Zan fara daukar sabon fim dina kwanan nan, zan fara daukar fim na Ingilishi mai suna ‘Accidental Husband’, fim din zai kunshi jarumai daga Kannywood da Nollywood. A Kannywood akwai jarumai irin su Ali Nuhu da Yakubu Mohammed, a Nollywood kuwa akwai Aled Ekubo da kuma Ini Edo.

Sources: Aminiya.com



©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top