ISLAMIC MEDICAL CENTER

  ••••| BASIR GA "YA MACE |••••

> basir na daurewar ciki - ta yawaita cin ya'yan itatuwa kamar lemon ๐Ÿ‹ Zaki taci har dusa da fatar ciki.

> shan kankana ๐Ÿ‰ ta dinga taunewa har kwallon ciki.

> cin ganyen salad bayan ta warke soaai ta yanka tumatur ๐Ÿ… da yawa ta sa gishiri da magi da mai kadan ciki.

> yanka ganyen kabeji kina kwadawa kina ci ko ki zuba a kan abinci.

> yin miyar alayahu ko shuwaka ko ugu amma ta zuba ganyen da yawa a ciki.

> cin ganyen zogale ๐ŸŒฟ ko rama ๐Ÿƒ ko dinkin ko yadiya ko lamsir amma kar ta cika kuli-kuli da yawa a ciki.

> yawan shan ruwa sossai.

Ya dace kullum kici Kala daya ko biyu daga wannan abubuwan Dana lissafo.

○BASIR MAI TSURO KO MAI BURTSOWA SAI AN MAYAR DA HANNU KO MAI ZUBAR DA JINI○

¶ ki tafasa makuba da gishiri a ciki ki tace ki shiga ruwan da dumi ki zauna a ciki kamar Rabin awa, a kalla kiyi sau biyu a Rana.

¶ ki tafasa sassaken mangwaro da jar kanwa ki dinga sha.

¶ ki daka citta tayi laushi, dakakken garin bakar habbatussauda ki kwaba da zaitun ko zuma ki dinga matsawa a duburar.

¶ ko ki Tafi hospital dan wani basir din sai anyi aikin.

■•••••SHAFAR ALJANNU•••••■ 

∆ ki kasance duk sanda Zaki kwanta ki dinga daura alwala.

∆ ki yawaita yin istigfari hailala da salatin annabi ( S A W) 

∆ ki karkade shimfidar kafin ki kwanta sannan ki karanta ayatul kursiyyu da falaki da nas.

∆ ki kwanta da barin hannunki na dama kiyi ta maimaita ayatul kursiyyu har bacci.

SINADARAN TABBATUWAR NI'IMA DA ZAMA CIKAKKIYAR MOWAR GIDA.

= BUSASSHIYAR MACE:

¶ sassaken baure.
¶ ruwan rake.
¶ ya'yan zogale.
¶ ruwan zuma.
¶ ruwan dabino.

Ki daka sassaken baure ko ki barshi a sassaken sa, ki zuba ruwa cikin kofi daya, mai girman ( jug ) idan gari ne sai ki sa cokali biyar idan sassaken ne sai ki kintata kamar yadda idan kin daka zai ba ki cokali biyar din, ki Dora a wuta ya tafasa kamar awa guda, sannan ki sauke idan ya kwanta sai ki tace, sai ki zuba markadadden ruwan kankana kofi daya, ruwan rake ma kofi daya ruwan dabino ma kofi daya, zuma Rabin kofi garin ganyen zogale cokali biyu, sai ki Dora a kan wuta Yayi ta dahuwa sai ya dahu sosai , zai yi kauri amma ba kirtif ba, idan ya huce sai ki dinga shan Rabin kofi safe da yamma Zaki ban labari.

◇DAUKEWAR NI'IMA BAYAN HAIHUWA◇

๐Ÿ‰ sassaken kankana.
๐ŸŒฟ sassaken baure.
๐Ÿƒ ya'yan zogale.
→ idon zakara.
→ asuwaki mata.
→ ganyen kafi suga.

Ki hada ki dake ki tankade yayi laushi sossai ki dinga zuba cikin cokali abinci daya cikin madara shanu kofi daya ko cikin madarar ruwa gwangwani daya kina sha safe da yamma.

GYARAN JIKINMU TA KO INA YADDA ZAKI DINGA KYALLI.

MAGANIN KURAJE DA KYAU FUSKA.

∩••••••SABULUN KURAJE••••••∩

→ asef soap.
→ pharmaderlm soap.
→ kanwa.
→ jar dilka.
→ zuma.
→ lemon tsami

→ ki goga sabulun kowanne guda uku, sannan ki zuba kanwarki dakakkiya cikin karamin cokali, ki kwaba dilka da ruwan zafi cikin cokalin cin abincin daya ki zuba a ciki, ki matse lemon tsami daya a Kai kisa zuma cokali biyar ki hada ki kwaba sosai, ki lailaya sai ki dinga shafawa a fuskarki kamar ya rage minti biyar ko bakwai kafin ki shiga wanka idan kin shiga wankan sai ki kuma wanke fuskar da sabulun kamar sau uku ko sama da haka insha Allah idan kina yi duk kurajen fuskarki zasu mutu.

SABULUN FIDDA TABO

¶ misscoroline soap
¶ shary soap
¶ aloebera soap
¶ garin alkama
¶ zuma
¶ kanwarki kadan
¶ lemon tsami bari

Sai ki goga su ki zuba zuma a ciki da lemon tsami da kanwar ki kwaba. Ki dinga shafawa a fuskarki minti biyar kafin ki shiga wanka, idan kuma Zaki yi wanka da shi Zaki dinga wanke fuskarki.

•••••••∆•LALLEN FUKSA•∆••••••••

✿ฺ lalle

✿ kurkum

ฺ✿ฺ sukari

✿ฺ dilak

✿ฺ Zuma.

Sai ki kwaba ki shasshafe fuskarki da shi, kamar minti uku sai ki yi ta murje fuskarki ki mutsutstsuke ta har kunnuwanki idsn lallen ya marmashe sai ki je ki wanke fuskarki yana sa kyan fuska santsi da kyallin fuska.

       ~~|•• LALAN JIKI ••|~~

••• lalle
•• zuma
• madarar gari
• dilka
• kurkum
• sukari
•mahala
• nescafe
• kaninfari

Ki hada ki kwaba da lallen ki shafe jikinki da ita ko ina ki mutittsike idan ta dan bushe ta marmashe sai ki shiga wanka, kiyi wanka da sabulun Dana koya miki shima lallen jikin yana da kyau sossai yana sa taushi da kyalli da santsin fata.


════════════════════

*Islamic medical center*
*・ Sirrin・rike・โ„ณiji* 
*WhatsApp _Groupร‡hart_*
๐Ÿ“ณ +2348037538596



© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top