Wani bincike da wasu masana kimiyya suka yi akan gashin kare da gemun dan adam wanne yafi daukar cututtuka ya nuna cewa gashin gemun dan adam yafi yawan cutuka fiye dana kare.

Masanan daga jami'ar Hirslanden dake kasar Switzerland sun bayyana cewa sun dauki mutane 18 da karnuka 30 dan yin wannan bincike, sun kara da cewa bayan kammala bincikensu sun gano cewa duka mutanen da suka bincika na da kwayoyin cutar bakateriya a gashin gemunsu amma 23 cikin karnuka 30 din da suka dauka ne kawai keda cututukan a gashin jikinsu, wasu ma daga ciki yawan cutar be kai na gashin mutane ba.

Saidai da aka yi hira da wasu mutanen masu gemu sunce basu yadda da wancan bincike ba dan kuwa ta yaya za'ace kare dake birgima a gurare da dama da mutum ba zai iya ko takawa ba ace ya fi gemun mutum da kullun idan zai yi wanka sai ya wakeshi?

Wasu kuwa sunce binciken zai iya zama gaskiya saboda idan kana da gemu da gashin baki akwai irin abincin da zaka ci ya rika makale maka a gashin, dan haka sai an yi taka tsantsan.

Post a Comment

 
Top