Ba wai kawai lokacin sanyi ne gashi ke bukatar kula ta musamman ba, a lokacin zafi ma ya kamata mata su mayar da hankali wajen kula da gashinsu musamman ganin lokacin ana fama da gumi wanda gashi ma ba a bar shi a baya ba wajen yin gumi haka kuma idan gumin ya yi yawa shi ke haifar da warin kai.
Idan har ya kasance mace ba ta kula da gashinta a wannan lokaci to babu shakka gashin zai rika yin wari musamman a lokacin da ta shiga rana.
Haka kuma zafi yakan sa mata susar kai wanda hakan ke kawo tujewar kitso cikin kankanen lokaci.
Lura da ire-iren abubuwan da muka kawo a sama da wadansunsu za mu ga akwai bukatar daukar matakai a kan hakan don ganin an zauna cikin kula.
• A yawaita wanke gashi. Wannan ya hada da gyaran gashi wajen yin shamfo ta hanyar yin amfani da man shamfo ko kuma a wanke gashin haka kawai da ruwa da sabulun wankin gashi.
• A karanta shafa mai a gashi musamman man gashi mai maiko.
• A yawaita yin kitso hakan shi zai sa gashi ya rika samun iska, ma’ana iska ta rika shiga cikin gashin.
• Idan ana zaune a gida a rika bude gashin kai yana shan iska
© Sirrinrikemiji
Post a Comment