Sharar Fage:

Can cikin kuryar surkukin dakinta mai duhun gaske Harira ta labe ta na kuka kasa-kasa ita kwal cikin daki. 

Jin motsin shigowata ya sa ta mikewa da sauri tare da kokarin share hawayenta da nufin boye damuwarta, wanda ba ta san cewa na kwashi mintuna tsaye cikin duhu Ina jin kukanta da wasu maganganu da ta ke cikin kukan nata ba.

Ban bari ta wahalshe da kanta ko ni ba, kawai na dube ta na ce, “fada min me ya samu Larai?” Kukan ya sake subuce ma ta, lokaci guda ta fizgi hannuna ta sake kutsawa da mu cikin surkukin dakin nan nata, yayin da ta fara magana cikin rada.

“Ki tufa min asiri Jummai don Allah, Alhaji Mati ne makocinmu ya ja Larai ya yi ma ta fyade. Kin gan ta nan kwance ya lalata ta. Inda Allah ya taimake ni, babu wanda ya gan ta.” Ta haska min ita da tocilan.
Yarinya na kwance babu kyan gani. Wani bakin ciki ya tokaren zuciya. Cikin tashin hankali na dubi Harira na ce, “Me ki ke nufi da Allah ya tufa maki asiri babu wanda ya gan ta?”

Ta sake yin kasa da murya ta cigaba da magana, “Jummai ke kin san dai Alhaji Mati ya fi karfinmu, ba za mu iya shari’a da shi ba, sannan mu kanmu fasuwar maganar nan a garin nan abin kunyarmu ne, don wannan tabon ya dinga bin mu kenan har tattaba-kunnenmu, sannan kuma ita kanta Larai rayuwarta ta lalace kenan har abada, domin babu mai auren ta. Ke kin san halin garin nan namu, kila ma har a dandali sai an dinga sa mu a waka.” Ta yi shiru daidai inda ta sake barkewa da kuka mai ban tausayi.

Nan tsaye kafafuwana babu karfi na bi Harira da kallon tausayi, yayin da cikin zuciyata na ji wani takaici mai ciwo na tafasa a kan Alhaji Mati Attajiri a garin Kanye, dattijo dan kimanin shekaru 60, wanda ya keta mutuncin wannan karamar yarinya ’yar shekara 11, kuma saboda wata al’adar banza ta wannan kauyen wai ba za a furta maganar ba, don fitarwa da wannan yarinya hakki. A waje daya kuma wai kuma shi kansa Alhaji Matin a na ganin ya fi karfin hukumci…

“Hatta mahaifin Larai ba zan fadawa ba, saboda kar zafin zuciyarsa ya sa shi daukar matakin da zai bar ma na baya da kura. Ni dai na bar wa Allah. Alhaji Mati kuma Allah ya isa tsakanina da shi,” Harira ce ta katse min tunani na da wannan furuci nata da ya kara tunzuran zuciya…

Ginshiki:

Fyade wani mugun abu ne da ya zama ruwan dare a cikin al’umma a wannan karni da mu ke ciki. Duk da dai a shekarun baya ma akwai shin, sai dai bai fasu ya yawaita kamar yanzu ba. Babban abin takaicin a harkar fyade shi ne yadda ba a fitar da wani hukumci mai zafi da tsanani ga masu aikata shi ba, ga kuma uwa uba zalunci da ya dabaibaye al’amarin, ta inda kiri-kiri mutum zai aikata fyade, amma idan ya na da daurin gindi ko arziki za a dabaibaye zancen a kashe magana ba tare da daukar mataki ba, wanda yin hakan na daya daga dalilin karuwar yawaitar afkuwar al’amarin cikin al’umma.

A nan Ina kira ga al’umma a kan lallai su waye, su san hakkinsu, lallai su jajirce wajen nemar wa kansu hakki idan irin wannan abu ya afku, domin ta irin wannan jajircewar ne za mu yaki wannan fitina da kullum ke karuwa a cikin al’umma.

Sannan a bangaren iyaye su ma, su ne ke da mahimmiyar rawar takawa don yakar fyade. Hakan kuwa zai tabbatu ne kawai idan iyaye sun tsaya tsayin-daka wajen sauke hakkinsu a matsayinsu na iyaye, wato wajen kulawa da yaransu yadda ya kamata; daga matan har maza kuwa.

Dalilan Fyade:

Sai kuma bangaren shi kan sa fyaden me ke kawo shi? Kadan daga cikin silar kuwa su ne:

*Siyasa…

Tabbas a na samun yawaitar fyade a lokutan wutar siyasa, wanda hakan na da nasaba da wani kulli da miyagun bokaye ke wa ’yan siyasar wajen nuna mu su samun galabar mulkin nasu zai ta’allaka ne da samun karamar yarinya a yi ma ta fyade… Wa’iyazubillah!

*Tsafi…

Nan ma hakan abin ke faruwa a wajen neman biyan bukatar duniya sai a nuna lallai aikata wannan ta’asa na da joni da samun biyan bukatar, yayin da mutane idonsu ya rufe wurjanjan za su iya aikata komai domin bukatar kan nasu… Allah ya kare mu.

*Zaman cirani….

’Yan ciranin da ke baro iyalansu su taho neman kudi, su nemi soraye ko shaguna su yada zango, sau tari a kan samu wannan matsalar a tare da su, domin za su zo ne su yi zaman watanni ba sa tare da iyalansu. Don haka bukata na iya tasar mu su, su nemi mafita ta hanyar jan yara, don samun biyan bukatun nasu.

*Sakaci…

Shi ma ya na haifar da hakan sosai wajen barin yarinya yawaita shiga wajen mazan da ba maharramanta ba, watakila kuma da shiga mai bayyana jiki.

Hanyoyin Magance Fyade:

A matsayinku na iyaye lallai wajibin ku ne kulawa da wasu abubuwa kamar haka:

*Kaucewa sakin yara sakaka fita…

Wasu iyayen na da wannan babban sakacin wajen barin yaransu fita a duk lokacin da su ke so, yaro kuma ya fita ya dauki dogon lokaci, uwa na gida ta na harkokinta hankali kwance.

*Aiken dare…

Kawai iyaye sai da daddare za ki ga sun hau aiken yaro sayen sabulun wanki ko na wanke-wanke ko maganin sauro, wanda duk da rana ba a tuna an aika ba, wanda hakan ba daidai ba ne ga macen ko namiji. Lallai iyaye su sani indai aike ne na dare, to gara uba ya fita ya yo.

*Fita wasa waje…

Kawai yaro ga gidansu, duk bai ishe shi wasa ba wai sai ya fita waje wasa cikin maza da mata, wani lokacin ma ba a kofar gida ne wasan ba, can wani loko za a tafi.

*Fita makota…

Shi ma wannan na daya daga dabi’u marasa kyau, wato tura yara makota wasa, wai har ka ji uwa ma na cewa, “na tura ta, ko na tura su makota wasa na huta da kiriniya.” Kawai kin yi Baba na daka gemu na waje.

*Wasa da maza…

Barin cudanyar wasa tsakanin mata da maza ya na da mummunar illa ba wai kawai a bangaren fyade ba ma har da sauran abubuwa marasa dacewa.

*Barin yarinyarki ta kwakumi kowa…

Iyaye na kallo yarinyar su mace zata dinga kwakumar kowanne namiji da sunan wasa ko shi namijin da ba wani muharraminta ba zai cakume ta da sunan wasa.
*Bayar da rikon yarinyar ki ga kowanne namiji…

Sannan iyaye mata a wasu lokutan saboda kiwar raino sai ka ga kowanne tarkacen namiji daga almajiri ko samarin unguwa duk an dauki rikon yara an ba su.

*Barin yara fita da sutura mai bayyana jiki…

Wata uwar ma yarinyarta daga ita sai kamfai za ta bar ta ta fita waje tumbur.

Ire iren wadannan abubuwa na matukar bada gudunmawa wajen jawo fitinar fyade da yawaitarsu, wanda ya kamata a yi kokarin yakar su da karfin tuwo.

Kafin na karkare sharhina Ina kira da babbar murya ga iyaye wajen kula da sa ido ga yara, haka su guji boye batun fyade idan ya faru ga yaransu, saboda tunanin wai abin kunya ne a gare su. Ko kadan abin ba haka ba ne fadar, domin daukar mataki shi ne zai kawo raguwar abin da yaduwarsa. 


© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top