(ALLAH SARKI RAYUWA!)

Wata Rana na sauka a wani Hotel, dake daya daga cikin jihohin da nake zuwa, tarukan kungiya, da yammaci na sauka bayan na gama kintsawa acikin Dakina Sai na fito na zauna a harabar Hotel Din saboda wannan yana daya daga cikin Al,adata saboda Ina qaruwa da abubuwan mamaki ko Al,ajabi ko kuma nishadi, kowa yana yadda yaga dama saboda duk mai sauka a Hotel ya san da irin wannan tsarin.

Ina zaune can sai idanu na ya kai kan wata kyakkyawar matashiyar budurwa, mazajen bariki kowa Yana gabatar da kansa, gaskiya yarinyar nan tana da matukar kyau, aqallah na kwana a Hotel yafi guda dari biyu, tun da nake ban taba jin wata karuwa ta burgeni ba sai wannan kyakkyawar budurwa, gata fara gata doguwa, matashiyar budurwa, amman gata acikin tsakiyar karuwanci.

Na fi minti Goma ina son su tafi amman samarin sunqi tafiya.
Can kamar misalin Sha biyu na fito Sai na hangeta zata fita, ban san lokacin da nace da ita, "kanwata har zaki fita?

Ga mamaki na Sai naga tayi murmushi tace yayana, ai bana kwana anan kullum"

Nace saboda me? tace saboda idan ban samu wanda ya biya kudin dakin da zamu kwana ba fita nake wani wurin ko za,a dace!!

Kawai Sai tausayin ta ya kamani, nace mata muje in biya miki daki ki kwana Amman fa ke kadai, tace haba yaya na sai dai mu kwana tare, babu yadda banyi ba amman tace sai dai mu kwana tare, bansan san da nace mata na amince ba.

Muka je na biya kudin dakin kwana daya nata, na dawo dakinta, muna ta hira har karfe, biyu na dare, akallah munfi awanni muna hira, can wajen karfe biyu da rabi Sai na dafe cikina Ina nishin karya, nace mata, ciwona ne ya motsa, haka ta rakoni har dakina tare da tausaya min.

Ai kuwa ana kiran Sallar asubahi sai gata a dakina, anan tayi Sallar asubahi, Wallahi idan kaji nutsuwarta idan tana karatun Alkur, Ani sai ka tausaya wa rayuwarta.

Tare muka karya, sai kace wacce muka jima da haÉ—uwa, tausayin ta ya kamani kwarai, na ce mata yanzu idan bata samu wanda zasu kwana ba yaya take yi?

Sai tace mun akwai wasu gayu da take zuwa unguwarsu kyauta suke kwana.

Na tausaya Mata kwarai da gaske, na tambayeta sunanta da garinsu, Bata É“oye min komai ba.

Na gaya mata waye ni da kuma suna na, Sai dai gaskiya ban gaya mata sunan jihata da kuma sunana na asali ba saboda wasu dalilai...

Ta zayyana mun labarinta, ta gaya mun dalilin ta na zuwa wannan jiha da kuma sanadin shigarta karuwanci!

Tsautsayi da kaddara ce ta shigar dani karuwanci, sanadiyyar wata qawata, inada haddar Alqur'ani akai na, saboda na samu gatan iyayena.

Lokacin da zamu rubuta jarrabawar qualifying, ban ci ba, Ina zaton danne min akayi saboda inada kokarina daidai gwagwardo, mahaifina ya rasu da jimawa, mahaifiya ta bata da karfin da zata biya mun kudin jarrabawar, babban abin takaicin shine dukkan kawayena sun samu nasara, na rasa inda zan saka kaina.

Babu inda ban nemi mafuta ba amman na rasa samun mai biya mun, dukkan masu kuÉ—in unguwarmu babu wanda ban bi ba akan su taimaka min amman sai suka gaza biya mun.

Akwai wata qawata ita ce ta hadani da wani saurayi, take ya biya mun kudin, gami da yi mun alheri iri iri.

Abin ka da kaddara, sai yayi Alkawarin aure na, amman da sharadin sai na saki jiki dashi, haka ko aka yi bansan kaddarar da tasa har yayi mun ciki ba, sannu sannu sai ga ciki ya bayyana, har aka fara surutai.

Aka tambaye ni wanda yayi mun na nuna shi, take ya amince da cewar cikinsa ne, yayi Alkawarin Aurena, iyayensa suka ce atafau basu yarda ba, suka ce sharri zan yi masa, ina ji Ina gani maganar Aure ta lalace, saboda bamu da gata, sannu sannu mutanen unguwa suka tsane ni, suka uzzurawa rayuwa ta.

Bayan watanni biyu shi wanda yayi mun cikin Allah yayi masa rasuwa, ni kuma bayan watanni hudu Sai na haifi yaro namiji amman bai zo da rai ba ya rasu!.

Bayan na haihu na nemi gafarar iyayena da dukkan Wanda na batawa, amman Wallahi duk da haka mutanen unguwarmu suka tsangwameni, sau biyu ana samun ranar aure ana fasawa, saboda ko na samu mijin Aure, Sai mutanen unguwarmu suje suyi tsurku su rusa auren suce wai na taɓa yin cikin shege!

Haka na rayu cikin kaskanci da wulakancin mutanen unguwar mu kuma da ace an taimaki rayuwata tunda fari da ba,azo wannan matakin ba yanzu.

Gaskiya ina da masifar son Aure, na sami damuwa kwarai da gaske.

Wannan tasa na yanke shawarar guduwa, wannan jihar, yau watana Tara a wannan jihar."

Lokacin da ta gama bani labarin fuskar ta cike da hawaye, na ce mata yanzu idan kika samu mijin Aure zakiyi auren, tace mun Wallahi zata yi amman da zan aure ta Wallahi ni za ta aura, ban san san da nace mata zan aure ki ba.

Washe gari muka sake Hotel saboda wasu dalilai, Hotel din da muka koma nace musu matata ce saboda gidan yana da tsari.
Kwanan mu biyu muka shirya batun Aure, nace zanje Inga mahaifanta, akwai wani Abokina a jiharsu, Wanda matarsa ta rasu, na kirawo shi na zayyana Masa komai, mutum ne mai fahimta da saukin kai tare da tausayawa Alumma,
Washe gari muka rankaya sai jiharsu amman sai da mukaje gidan su wannan abokin nawa acan ma muka kwana saboda dare.

Na Gaya Masa cewar nayi Alkawarin zan aure ta amman zancen gaskiya bani da halin auren Mata biyu, saboda baifi wata uku bikina ba a wannan lokacin.

Muka hada wani plan ni da shi.
Da safe muka gaisa na gabatar dashi agurin ta, nace mata duk duniya bani da amini sama dashi.

Misalin karfe Tara mukaje gidan su, Mahaifiyarta ta cika da murna, akayi maganar girma tare da cewar zan aureta.

Ban bar garinba Sai na bata karamar waya, sannan na samu sabon layi na bata, wannan abokin nawa yayi musu Alheri Mai yawan gaske.

Muka rabu cikin yanayi Mai cike da ban tausayi, lokaci zuwa, lokaci wannan abokin nawa dake jihar su yana zuwa wurin ta su gaisa, harma suka shaqu suka zamto kamar Aminan juna.

Anyi sa'a ta mika dukkan lamuranta ga Allah, kullum bata da aiki sai ibada da kuma neman gafarar ubangiji.

Lokaci zuwa lokaci duk da ina da karamin karfi na kan tura musu da abinda ubangiji ya hore min duk saboda in kwantar mata da hankali saboda munyi Alkawarin Aure,
duk abinda zan bata wannan abokin nawa shine yake kai mata.

Kusan kullum muna shafe awanni biyu ko uku muna waya domin wata rana har karfe biyun dare muna waya Ina qara kwantar Mata da hankalin ta akan ina nan Ina shirya mana bikin mu.

A gefe daya kuma Wallahi bazan iya aurenta ba, saboda biki na bai fi watanni uku ba.

Bayan sati biyu naje jiharsu mukayi wa iyayenta Goma ta Arziki, tare da Alkawarin zan turo da magabata na bayan sati biyu.

Kafin in tafi muka yi magana ta fuskarta juna da wannan aboki nawa, inda ya nuna min Wallahi yana son ta zai aure ta kuma zai rike ta cikin mutuntaka da Amana.

Muka shirya wani plan cewar bayan sati daya zai ce mata ALLAH yayi mini rasuwa.

Haka ko akayi bayan kwanaki aka ce mata bani da lafiya, idan muna waya har kukan tausaya min take yi ni kuma Sai na koma kamar mara lafiyar Ina cewa ta yafe mun idan nayi mata laifi.

Bayan kwanaki kadan Sai wannan Aboki nawa ya sanar musu da rasuwata.

Ni a jihar Kano nake amman sai nace mata a jihar Kaduna nake.

Tayi kuka kamar ranta zai futa, tayi kuka iya kuka, domin har kusan shidewa take yi idan tana kuka, idanun ta suka kumbura ta koma wani yanayi.

Dukkan wanda ya sanni da wani layin Glo,. Mai lambar 080557811** tun da aka ce na rasu na dena amfani da layin saboda ita ma dashi take kira na.

Sannu sannu wannan Aboki nawa yana kwantar mata da hankali tare da yi mata nasihohi,
cikin Ikon Allah, har yace zai aureta zai maye gurbi na.

Haka ko akayi, tazarar Aurena da nasu sati uku ne kawai, aka kaita gidansa ya riketa rikon Aminci da nasara.

Ya kyautatawa rayuwarta, da yake gidan da yake akwai baranda, babba da kuma gareji, sai ta bude makarantar karatun Alkur,Ani Mai girma, inda "yammata da yara suke zuwa, kafin kace menene wannan ubangiji ya albarkaci wannan makaranta.

Zancen nan da nake muku haihuwarta biyu duk tagwaye maza, suna nan cikin kwanciyar hankali da kosasshiyar lafiya.

Har yanzu bata san Ina raye ba, har yanzu bata san plan muka hadaba da mijinta, ina nan zan shammaceta wata rana muje har jihar ni da iyalina da "yayana domin ganawa da junanmu.

DARASIN DA ZAMU DUBA

(1) Mafi yawancin wadanda ke yawon karuwanci da zamu yi bincike da mun nemo musu mafuta.

(2) Shin me yasa mutanen unguwa wasu basa taimakon, makwabtansu, shin da ace an tallafawa wannan budurwa zata shigo karuwanci har wani ya yaudareta yayi Mata ciki?

(3)yanzu da bamu haduba ba shikenan a haka zata rayu cikin kazamin karuwanci?

(4) Shin da bata tuba ba shikenan anyi asarar hafizar Alkur,Ani kenan?

(5) Shin menene yasa Al,ummarmu ke tozarta wanda yayi laifi yace ya tuba? Shin mu bama aikata laifin kenan mu tuba?
(6) shin me yasa mutanen unguwar su suka tozarta ta, saboda tayi cikin shege, me yasa ba,a zargi wanda ya yaudare ta yayi Mata cikin?

Ya kamata mu kula da hakkin makwabtaka, mu dinga agazawa Wanda ya Gaza, mu dai na manta Alherin mutum mu bijiro da sharrinsa.

Idan akace ga lalatacce a unguwarmu kada mu tozarta shi mu fara saurarar uzirinsa kafin mu yanke hukunci.

Ubangiji ka ganar damu.

Koda yaushe so nake na taimakawa wanda ya bar hanya madaidaciya na bashi shawara da gudun mawa wajan gyara goban sa.
#copied


© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top