Kowane magidanci yana son ya mallaki zuciyar matarsa, domin samun kwanciyar hankali a cikin gidansa. Sai dai kuma ba kowa wani magida ne ya san yadda zai mallaki zuciyar matarsa ba. Lallai magidanta bayan da za su samu mallakar zuciyar matayensu, sai dai idan sun tsare hakkokin da ya rataya a kansu. Hakika akwai hakkoki masu yawa wadanda Allah ya daura wa duk wani magidanci a kan matarsa, kamar hakkin ciyarwa, wajen zama, karantarwa, tufatarwa da dai sauran su. Idan magidanci ya kasa daukar dawainiyar iyalansa, to ba zai taba samun kwanciyar hankali ba a cikin gidansa. Ita mace tana bukatar a koda yaushe tana bukatar mijinta ya biya mata bukatocinta a duk lokacin da ta bukata. Idan ta kasa samun haka kuma, to babu wani abun da mijin nan nata zai yi ya burgeta. Mata kadan ne suke da tausayin mazajensu idan ba su da shi. Kuma ita mace tana iya fada wa mijinta cewa, me ye ka taba yi min, komin kokarin miji zai iya fuskantar wannan matsala. Babu wani magidanci da ya fi karfin matarsa, sai dai wanda Allah ya ba shi ta kwarai wacce take jin tsoron Allah.
Magidanci zai iya mallakar zuciyar matarsa ce ta hanyar tarbiyartar da ita kamar yadda addini ya tsara. Sannan kuma magidanci ya yi kokarin sauke duk wani nauyin da ya rataya a kansa wanda Allah ya dora masa. Ta wannan hanya ce kadai magidanci zai iya mallakar zuciyar matarsa. Tana mai bai wa magidanta shawara da su tunga kokarin sauke nauyin da ya rataya a wuyansu na hakkin iyalansu, idan suna son samun natsuwa a cikin gidajensu. Ya kamata magidanta su karanci yadda za su sauke hakkin iyalansu, domin dole ne magidanci ya karanci yadda zai sauke hakkin iyalansa.


© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top