Wannan wasikarwani mijin barauniya daya turo mana ne. Mu sha karatu lafiya. Da fatan zan a fahimci darasin dake kunshe cikin wannan labarin.

A wani dakin cin abinci muka hadu. Mun hadu wajen biyan kudi. Su uku ne ita da abokanta muma mu uku ne ni da abokaina muna kan hanyarmu na zuwa babban birnin trayya ne.

A gaskiya kyauta ne ya soma dauke mini hankali. Gata kuma da zazzakar murya. Ta sha duguwar riga har kasa kuma ta rufe kanta baka iya ganin gashin kanta sai dai farar fuskanta kawai ke haskawa a bakar jallabiyar data saka.

Na samu damar shawo kanta ne bayan na biyamusu kudin abimcin da suka ci. Na kuma jata gefe muka yi hira na gabatar mata da kaina a matsayin bako kuma wanda yake kan hanya. Muka yi musanyar lambobin mu na kama hanya suma haka.

Daga wannan lokacin muka rika kiran juna muna soyayya ina kuma zuwa wurinta a duk lokacinda hali ya samu ko kuma idan zan wuce Abuja.
Cikin watanni shida muka yi aure na kawota garinmu na ajiyeta. Ban hadata da matata ba gida guda na waremata a kuma daya daga cikin manyan unguwannin garinmu. Duk wasu kayan alatu na rayuwa tunda Allah Ya horemini na tanadar mata. Muna zaune lafiya babu wani matsala sai dai fa ban isa nayi ajiyan kudi bama a dakinta duk inda na boye kudi idai a gidan tane to kudai amini zare ko kuma a sakesu gaba daya.
Ban taba tunanin matata bace ke mini sata. Na kori masu gadina yafi a kirga. Mun bata da 'yan uwana na jini da abokaina na kusa akan zarginsu da sata.
Ranar da mahaifiyata tazo gidana ranan aka sace mini naira miliyan 15. Kuma wannan ranar na fahimci cewa babu mai yi mini sata sai matata.
Nayi ajiyar kudin har naira miliyan 30, amma washegari dana zo zan daukesu sai naga babu rabinsu. Kuma banda mahaifiyat da matata babu wanda ya shigo mini gida a awannin dana ajiye wannan kudin da kuma lokacin da na bukacesu. Nayi juyin duniyan nan tace sam ita batasan zancen ba. Asali ma ina sone na lakabamata sata. Haka na hakura ko mahaifiyarmu banyiwa zancen ba na dauki lamarin na barwa Allah.
A bayi ko mako guda ba wani ranar lahadi da misali karfe 4 na yamma sai ga abokina ya kirani a waya yana nemana na zowa wani shagon super Market babba dake garinmu. Ina zuwa da kyar na gane matata saboda Dan Karen dukan da aka mata tayi sata a shagon. Da yake masu shagon sun sanni na basu hakuri na karbeta na kaita asibiti aka mata magani. 
Abun mamaki da karfin hali irin na barauniya taki sam wai sharri ake mata ita bata saci komai ba. 
Anyi haka da kamar makwanni 2 sai gashin an mata duka kamar bazarayi rai ba a wani gidan buki ta satar musu waya. Ta dawo gida duk fiska a kumbure tace hadari sukayi.
Malam Tonga kada na cikaka da dogon jawabi yanzu haka tana prison an yanke mata hukuncin zaman yari na shekaru uku saboda samunta da satan kayan kwaliyan gwalagwale data je har wata jiha ana buki ta shiga ita da wadannan kawayen nata suka yi. Sau biyu na yin bari saboda dukan datake ci a wajen sata. Na gode Allah ban haihu da ita ba. Ranar da aka yanke mata hukuncin dauri ranar nayi mata saki.
Irin kaskanci, wulakanci, tozarci da abun kuyar dana shiga ko na gani saboda skacin rashin binciken da banyi ba na auro barauniya. Wallahi gara ace tsohuwar karuwa na auro. Allah Ya albarkacemu da mata na gari.

Ko wani darasi mai karatu a dauka a wannan labarin?


© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top