Wata matar aure, mai shekaru 29, ta garzaya kotu a kasar Saudiyya domin neman a raba aurenta da mijinta saboda tsananin son ta da ya ke yi.

Mijin matar ya bayyana cewa bai san dalilin da yasa ta ke bukatar ya sake ta ba duk da irin soyayyar da ya ke nuna mata da kuma irin sadaukarwarsa gare ta.

Matar ta kafe a kan cewa mijin na ta sai ya sake ta duk da cewar bai taba hana ta wani abu ba, amma ta bayyana cewa ta nemi ya sake ta ne saboda ya daukake ta fiye da mahaifiyarsa.

"Ba zan taba yarda da mutumin da zai ba ni duk abinda na ke so ba amma ya gaza yi wa mahaifiyarsa komai ba koda kuwa ta nemi ya yi mata," ta shaida wa alkali.

Ba a bayyana sunan matar ko mijin ba. Mijin, wanda ya yi matukar girgiza, ya shaida wa alkalin kotun cewa ba ya son rabuwa da matarsa a saboda haka ya ce bai amince da bukatar ta ba.


Matar ta amince cewa mijinta na kashe kudade masu yawa a kan ta, ya dauke ta zuwa kasashen ketare tare da siya mata kaya masu tsada matukar ta na so, amma ta ce duk da hakan ba ta son cigaba da zama da shi.

"Ba zan iya yarda da mutmin da ba ya kyautata wa mahaifiyarsa ba. Ni ma zai iya juya min baya a kowanne lokaci," a cewar ta.

Mijin ya tambaye ta cikin mamaki, "me yasa za ki bar ni duk da na bar dangina saboda ke?"

Ita kuma ta bashi amsa da cewa, "tabbas ka yi gaskiya, kuma hakan ne yasa na ke so ka sake ni."

Daga bisani matar ta dawowa da alkali kudin sadakin da mijinta ya biya, kuma alkalin kotun ya raba aurensu.

®Legit

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top