Daga Mahmud Isa Yola

Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau yayi kira ga hukumomin da suke hidimar Alhazai a Nijeriya da su kiyaye Amanar da Allah SWT ya daura musu ta hanyar gudanar da aikin su tare da baiwa Alhazai hakkokin su yayin ibada.

Sheikh Bala Lau ya yi gargadin ne yayin da yake zantawa da 'yan jarida jim kadan bayan ya jagoranci Sallah Jumma'a a Yola, inda yayi Khudubah akan aikin Hajji da hukunce hukunce ta.

Shehin malamin yace amana ne babba akan dukkan masu hidmar Alhazai na su tabbatar da cewa Alhazai sun gudanar da ibada cikin walwala ba cikin kunci ba.

Yace dole ne a tabbatar ba'a zalunci kowa ba, tun daga tafiya har zuwa masaukai da kuma dawowa gida. Sheikh Yace yakamata hukumar Alhazai ta sanya ido kan kamfanonin da suke jigilar alhazai da masu kula da masaukan su, don tabbatar da cewa kowani mahajjaci ya samu hakkin sa.

"Wannan amana ne a kan su. Kuma su sani cewa Manzon Allah SAW ya fada a hadisi ingantacce cewa Allah SWT zai tambaye mu akan amanar da aka daura mana." inji Sheikh Bala Lau.

Malamin ya kuma yi fatan alkhairi ga hukumar alhazan na Nijeriya da kasar Saudiyya da ita ma take iya kokarin ta wajen tabbatar da mahajjata sun gudanar da ibada ba tare da muzgunawa ba.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top