Duk kyawun ki ta fuska, ta jiki, ilimin ki, dukiyar ki, na iyayen ki ko sarautar ku, idan baki da riko da addini ba ki da kyawun hali, to kin rasa kima da mutunci a idon mijin ki, duk soyayyar da yake miki to wata rana dole ya ragu koma ya rabu dake, ki sani zai faɗa a soyayyar ki ta wa'encan abunda na lissafo a sama amma soyayyarki za ta tabbatu ne idan kina da kyawun hali, kina da biyayya kin ɗauke shi a matsayin shugaba kuma aljannar ki, ranar da kuwa ya samu wacce ta haɗa duk abubuwan da na ambata ga kuma riko da addini , kyawun hali, ko da bata ma haɗa ba, to ta karɓe zuciyar kenan har abada, dan haka ki zamo mai riko da addini da kyawawan hali sai ki zamo sarauniyar uwar gida
Dayawan iyayen mu a yanzu suna cutar damu, su kuma suna ɗauka wai suna ceton mu ne daga wulakancin ɗa namiji, idan muka fara girma ba zasu dunga yi mana nasihar idan muka yi aure ya zamu zauna da mijin mu ko ya zamu fuskanci wa'enda suka zo neman auren mu ba, a'a kawai huɗuba suke mana yadda zamu musu kalamai masu daɗi mu rage kunya, ko in kunyi aure yadda zamu iya tarairayar miji da kwanciya da shi, haɗa kayan mata ko a faɗa mana inda ake siyar da kayan mata, kuma sai su kara da cewa namiji ba amana idan baki iya wa'ennan ba wallahi shikenan, kuma kada kiyi masa sanya da dai sauran su.
Su kuma fa iyayen nan namu da suka fara girma iyayen su, sun fara koyar da su ne tarbiyyar ya'ya idan mutum yazo neman auren su za su fuskance shi, kuma kullum huɗuba ake musu su riki kunya, tsafta, biyayya da kyawawan hali a gidan miji, sai yarinya jibi ko gobe auren ta za'a samu tsoffofi ko yan'uwa masu daraja su faɗa mata menene aure kuma ya za tayi ta riki mijin ta, me za ta dunga ci ko sha domin mijin ta ya kara samun nutsuwa da ita, kuma a faɗa mata ta riki addu'a.
Amma a yanzu sai ma amarya a fara shagulgulan biki sati ɗaya bata ma zauna da manyan ta ba, ita de daga ita sai kawaye ana gun party dasauran su, koma ba patin ba tana wasu sungullolin ta, kuma aure saura wata ɗaya ko watanni maganin mata kawai za'a yi ta ɗura mata, kuma abun bakin cikin magungunan mata ɗinnan na tada sha'awa in ba'a yi hankali ba ko tsakanin ta da wanda za ta aura mai afkuwa ta afku ko tsakanin ta da wani, ko tsakanin ta da kawa. ALLAH tsare mu.
Duk iya gadon ki, haɗa maganin matan ki, miji zai iya rabuwa dake matukar baki da riko da addini, kyawawan hali, baki da biyayya, kyawun ki zai iya kaiki ki auri namiji mai dukiya mulki da sauran su, abunda zai dauwamar dake a zuciyar shi da gidan kyawawan halinki, biyayya da sauran su, kyawun ki zai sanya shi faɗawa soyayya dake amma kyawun halin ki zai dauwamar da sonki har ya zamo kauna har abada kenan har ya koma ga ALLAH yana sonki yana yabon ki yana kuma sanya miki albarka yana yiwa iyayen ki addu'a ga kuma kyautata wa domin duk namiji da kike ma biyayya za kiga kyautata wa kullum kuma zai so farin cikin ki.
Iya kwanciyar ki zai sanya shi shiga hali na jindaɗi a lokacin amma ba zai iya dauwamar da soyayyar ki ba ko natsuwa da ke a zuciyar shi ba, iya kwanciyar ki zai iya sanya shi kasancewa da ke tsawon dare amma ba tsawon rayuwa ba.
Mafita a gare ki, ki zamo mai riko da addini, tsafta, biyayya, kyautatawa, kyawun hali, kuma ki zamo ma'abociyar soyayya, kwanciya da sauran su, kada kuma ki zamo mai kwashe kwashen maganin mata domin samun lafiyar ki da mijin ki, akwai wa'enda malamai suka koyar to jeki nemi wa'azozin ki koya, domin bincike ya nuna wa'encan da ake sayarwa dayawa suna jawo cututtuka masu tsanani kamar cancer da kashe asalin ni'imar mace ko namiji da wasu cututtuka ɗin.
✍🏽 Rasheedah Bintu Abeebakar (Daughter of Islam)
© Sirrinrikemiji
Post a Comment