Dan wasan gaba na Manchester City Riyad Mahrez ya yi nasarar daga ragar Najeriya a bugun tazara a cikin minti na karshe wanda hakan ya sa Aljeriya ta yi waje da Najeriya 2-1, ta kai wasan karshe na gasar cin kofin kasashen Afirka na wannan shekara ta 2019, da ake yi a kasar Masar.
Bal din da dan wasan ya ci daidai da tashi ta sa magoya bayan tawagar ta Aljeriya su kusan 7000 da ke filin wasan suka barke da sowa, kasancewar kasar tasu ta yi waje da Najeriya ke nan ta kai wasan na karshe da za su yi da Senegal ranar Juma'a.
Tun da farko Aljeriya ce ta fara cin Najeriya bayan da dan wasan Super Eagles din na baya William Troost-Ekong ya ci gidansu bisa kuskure, bayan da Riyad Mahrez din ya sheko wata bal daga gefe.
Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci ne a minti na 72, Ighalo ya farke wa Najeriya da bugun fanareti.
A karawar farko da aka yi ta daya wasan na kusa da karshe tsakanin Senegal da Tunisiya a ranar Lahadin nan, Senegal ta yi nasara da ci 1-0, wanda hakan ya sa ta kai wasan karshen da za ta hadu da Aljeriya a ranar Juma'a 19 ga watan Yuli.
Yan Najeriya da dama sun nuna rashin jin dadin su bisa rashin sumun nasarar yan kwallon Najeriya, yayin da cece-kuce suka yi yawa na cewa duk sanda suka saka wannan jesin basu samun nasarar tashi da wasan.
Shin kuna ganin da gaske ne jesin ce ka kowa wa yan wasan kwallon kafar Najeriya faduwar wasan?
©HausaLoaded
Post a Comment