Da yake Magana da manema labarai bayan kallon wasan, Dr. Shamsuddeen Mai Yasin ya nuna jin dadi kan fim din barkwancin inda ya bayyana shi a matsayin wasan barkwanci na Hausa da ya cancanci samun lambar yabo.
A cewarsa, wasa ne da aka yi shi da sigar barkwanci amma akwai sakonni da jawabai da dama tattare dashi tare da darasi mai amfani sosai.
Wasan na kunshe da manyan jarumai irinsu Ali Nuhu, Sulaiman Bosho, Rabi’u Daushe, Hadiza Gabon, Aminu Momo,Falalu A Dorayi.
Wakili ya kasance fim din bakwanci na Hausa da ke nuna al’adu da dabi’un wasu shugabannin al’umma yayinda suke gudanar da ayyukan da ya rataya a wuyansu. Ya kuma nuna yadda tsarauta take ta sigar barkwanci domin nishadantar da masoya.
An tattaro cewa an shirya fim din ne wanda Darakta Falalu A Dorayi ya shirya tare da hadin gwiwar masarautar Zaria karkashin jagoranin mai martaba Alhaji Shehu Idris.
©HausaLoaded
Post a Comment