Mahaifiyar Fitaccen Ɗan Wasan Ƙwallon Ƙafa na ƙungiyar Super Eagles wato marigayi Rashidi Yekini ta fara siyar da biredi a garin Ila da ke jihar Kwara
Tun da farko wasu Rahotanni sun bayyana cewa tun bayan rasuwar ɗan na ta ne mahaifiyarsa tare da iyalansa suka shiga halin matsin rayuwa, wanda hakan ta sanya ta kama sana'ar sayar da biredi domin samun abin da zai tallafi rayuwarsu.
Wasu rahotanni da majiyarmu ta samu sun bayyana cewa iyalin tsohon ɗan wasan su na fama da matsin rayuwa, domin har an jiyo muryar mahaifiyar ta sa tana neman taimako sabo da irin halin matsin da su ke ciki.
Idan za'a iya tunawa dai Rashid Yekini a lokacin rayuwarsa ya samu nasarar zura ƙwallaye 37 a cikin wasanni 58 da ya bugawa ƙasar nan a ƙungiyarsa ta Super Eagles, kuma ya kasance ɗan wasa mafi yawan ƙwallaye a ƙungiyar.
Ya kuma jagoranci ƙungiyarsa a wasu manyan wasanni guda biyar waɗanda su ka haɗar da cin kwallon Kafa a kasar Amurka a shekarar 1994 da wanda aka gudanar a ƙasar Faransa 98.
Ko ya Tsaffin 'yan Wasan Ketare su ke?
©HausaLoaded
Post a Comment