• Cigaban Rubutu Domin Maza

Dukkanmu mun taso mun samu ana cewa mata sun kasu gida uku game da lamarin kwanciya: akwai harija, mutawassida da dakhila. Ta tsakiyar ce ta fi yawa a rahotannin baka. Marubucin nan bai da tabbas game da wannan bayani a ilmance. Amma dai maganar ba ta yi nesa da abin da gogayyar yau da kullum take tabbatarwa ba.

Gazawa ce a bangaren namiji, ko ma a wane rukuni matarsa ta fada a cikin biyun qarshen nan, a ce ba ya iya gamsar da ita a wurin kwanciya. Kazalika qalubale ne a gare shi, idan matar ta kasance cikin rukunin farko, dolensa ya zaqulo yadda zai gamsar da ita. To me da me ke sa mutum ya iya gamsarwar?

Farko, akwai buqatar bahaushe ya gane cewa ba fa zallan dukhuli ne ke gamsar da mace ba, sai ya riqa hadawa da nau’in “romance” din da matar ke buqata. Mata da yawa na qorafin wannan jahilci nasa. Binciken masana harkar ya bayyana cewa, ko minti biyar kawai miji zai yi a duhuli, amma ya yi “romance” da matarsa na kimanin awa guda, za ta gamsu. Wane irin “romance” ne mata ke buqata?

Kowace mace na da irin nata. Nuna shauqi da tattaunawa cikin qauna ke ba mace damar bayyana wa miji yadda take da abin da take buqatar. Abokina kada ka qi farar da irin wannan tattaunawa, don amfaninka, kuma kariyar matarka ce daga shedanun zamani. 

Na biyu, ya rage wa kansa matsalolin rayuwa, domin gwargwadon natsuwar zuciyarsa, gwargwadon kuzari da isasshen lokacin da zai samu wurin gamsarwar. Yadda nauyin matsala ke tsofar da mutum, haka nauyinta ke hana shi katabus a kwanciya. Don haka kulawar taka ce abokina. 

Na uku, Ya kula da lafiyarsa. Hakan kuma yana farawa ne tun daga nau’in abincin da mutum ke ci, zuwa motsa jikin da yake yi. In har aka kiyaye, masana sun ce za a zauna cikin qoshin lafiya. Alaji ka kashe kudi ka ci abinci mai inganci, kuma ka sha kayan marmari dangin kankana da mangwaro. In babu isassun kudi, ka ci abinci isasshe mai gina jiki. Misali tuwo da miyar kuka wadanda suka dahu sosai. Ka daina ciye-ciyen nan na zamani a matsayin abinci. Zauna sosai ka yi hani’an da tuwo ko shinkafa da wake da ganye. Sannan ka tambayi qwararru kan wane irin motsa jiki ya dace da kai. Insha Allahu in ka riqe hakan, za ka ga kana gamsarwa ko da ba ka sha magani ba. Kuma dama ba ka buqatar shaye-shayen magungunan nan domin wata kiyayewar ta lafiya. 

A haqiqanin zance, ba ma buqatar a ma ce mana, rashin gamsar da matanmu gazawa ce babba daga bangarenmu, domin duk mun sani dama. Abin da muke buqatar fahimta shi ne, rashin gamsar da su din, daukar alhakinsu ne, wanda za mu amsa hakan a gobe qiyama, kuma ba su damar kula wasu mazan ne. Hakan kuma gurbata al’umma ce da bala’o’i.

• A yi haquri da ni na kasa sakin jiki da rubutun domin maudhu’in na da nauyi.

Muhammad Bin Ibrahim



© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top