Wata mata ta bayyana yadda ta dinga barin kanwarta tana kwanciya da mijinta ba tare da mijin ya sani ba

- Yanzu kuma abin yana damunta, kuma tana so kanwartan ta daina kwanciya da mijin nata, amma kuma ba ta so ta batawa kanwarta rai

- Ta bayyana cewa tun suna yara komai nasu tare suke yi tun, saboda haka ba ta ga dalilin da zai saka ta hanata kwanciya da mijinta ba

"Na tashi da kanwata a matsayin babbar kawata, muna yin komai tare, muna wasa tare, karatu tare, cin abinci tare, hatta abokanan mu daya ne a makaranta.

"Zaku iya kallon abun a matsayin bakon abu, amma ni da ita tagwaye ne, kuma ina ji da ita fiye da komai a rayuwata.

"Ban taba tunanin zan ji ina kaunar wani a rayuwata ba kamar May. Ba 'yar uwa bace a gurina kawai, ita ce babbar abokiya ta, ita ce na yadda na fadawa duk wasu sirri na. Ko bayan rabuwar mu da muka tafi makaranta abotarmu tana nan.

"Mun yi sabbin abokai sannan kuma mun ga yanayin rayuwa kala-kala, amma duk da haka muna fadawa junanmu duk abinda ya faru damu.

"Bayan mun gama karatu na hadu da Edmund, saurayin dana ji ina kauna sosai, wata uku da fara soyayyar mu ya nuna mini yana son aurena.

"Na sha fadawa Edmund cewar ina da 'yar uwa, amma kuma ranar da ya fara ganinta yayi mamakin yadda aka yi muka zama tamkar an tsaga kara, saboda babu wani banbanci.

"Muma kanmu munyi mamaki da muka ga cewa Edmund ba ya iya banbance mu, ya sha zuwa ya zauna da May a tunaninshi ni ce.

"May har wasa take yi take cewa Edmund ya auri duka mu biyun, amma a lokacin ban taba tunanin hakan za ta faru ba.



"Wata rana muna magana da May a waya sai take fada mini cewa tana son Edmund, kuma sosai, tana jin shi a zuciyarta sosai.

"Dama na san May za ta so Edmund saboda komai namu iri daya muke so, kuma ni da ita bamu taba boyewa junan mu sirri ba, shine ma yasa ma bata boye mini zancen ba.

"Hakan yasa na cewa May mu dinga raba Edmund ta yi soyayya dashi nima nayi, tunda ba iya gane mu yake ba.

"Ko a ranar auren mu ma, dana shiga na canja kaya, May ce ta fita taje wajen Edmund da kayan dana zo na saka, inda ni kuma na tsaya a cikin mutane a matsayin ita.

"Ba mu taba gayawa kowa abinda muke ba. Na ji dadi matuka lokacin dana ga Edmund yana sumbatar ta.

"Tun daga wannan lokacin, ni da May muka cigaba da kwanciya da Edmund lokaci zuwa lokaci, kuma mun yi alkawarin ba za mu taba gayawa kowa sirrinmu ba.

"Lokuta da dama ina jin rashin jin dadin yadda na bar Edmund a cikin duhu, ina son Edmund amma kuma gaskiya ina son May fiye dashi, kuma ina so ta zauna cikin farin ciki.

"Yanzu haka ina yin kishi ne, amma kuma bana so ran May ya baci, saboda ni ce na fara yadda da hakan."

® Legit

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top