Fitaccen tauraron fina-finan Kannywood, Sani Danja, ya yi zargin cewa hukumar tace fina-finan jihar Kano ta rufe kamfanin daukar hotonsa saboda siyasa.

Sai dai hukumar ta ce ta dauki matakin ne saboda kamfanin bai cika sharudanta na yin rijista ba.
Tauraron ya shahara wajen goyon bayan tsohon gwamnan jihar, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso da jam'iyyar PDP da ke hamayya a Kano, wanda ya raba gari da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje tun bayan zaben 2015.

A wata tattaunawa da ya yi da BBC, tauraron ya ce, "Babu wata maganar yin rijista, akwai da ma mutanen da ake hakonsu saboda dalilai na siyasa. Kuma ni ina gaya wa mutane cewa su rika ganewa bambancin siyasa alheri ne; idan kana abu wanda babu wanda zai kalubalance ka abubuwa ba za su tafi daidai ba."

Sani Danja ya ce sai da ya yi rijista da dukkan hukumomin da ke kula da harkokin kasuwanci kafin ya bude kamfanin daukar hoton, ciki har da Hukumar rijstar harkokin kasuwanci ta Najeriya, Corporate Affairs Commissioin.

Sai dai shugaban hukumar tace fina-finai ta Kano, Malam Isma'ila Na'abba Afakallah ya shaida wa BBC cewa ba makarkashiyar siyasa ce ta sanya suka rufe kamfanin tauraron ba, yana mai cewa rashin yin rijista ne.

"Babu wani gida[na daukar hoto] da muka rufe don yana daukar hoto; mai yiwuwa idan gidan daukar hoton wanda kake magana a kai [Sani Danja] ya fado cikin wadanda basu yi rijista ba, to an rufe shi."

Ya kara da cewa ba kamfanin daukar hoton Sani Danja kawai hukumar ta rufe ba, yana mai cewa sun rufe daruruwan gidajen daukar hoto da basu yi rijista ba, ba tare da la'akari da jam'iyyar siyasar da suke yi ba.

Masu sana'ar fina-finan Hausa da mawakan Kannywood da ke goyon bayan tsohon gwamnan Kano, Rabi'u Kwankwaso, sun sha kokawa da gwamnatin Ganduje saboda kama su da take yi saboda, a cewarsu, bambancin siyasa.

Ko da a watan Satumbar 2019, sai da hukumar ta tace fina-finan Kano ta sa 'yan sanda suka kama fitaccen mawakin nan Naziru M. Ahmed.

A wancan lokacin, 'yan sanda sun yi zargin cewa an kama mawakin ne "saboda kalaman batanci" da ya yi a cikin wasu wakokinsa.

Sai dai 'yan uwa da magoya bayansa sun yi zargin cewa an kama shi ne saboda alakarsa da Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II, mutumin da ya dade yana kai ruwa rana tsakaninsa da Gwamna Ganduje.

Rundunar 'yan sandan ta musanta zargin.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top