Wani mutum a jihar Nasarawa me suna Christopher Chori ya dirkawa surukarshi, Priscilla ciki a lokacin da ta je gidanshi dan mai renon jaririn da matarshi ta haifa.

Lamarin ya farune a jihar Taraba kamar yanda The Sun ta ruwaito inda Surukin Chori, Silvanus Kwange wanda tsohon sojane bayan mutuwar matarshi ta farko ya auro Priscilla, saidai sun kwashe shekaru 10 babbu haihuwa, lamarin da ya jawo cece-kuce tsakanin dangi inda ake zargin Priscilla da cewa itace bata haihuwa tunda Mr Kwange ya haihu da matarshi ta farko.

Priscilla da taimakon Surukinta,Chori ta nemi maganin haihuwa a asibiti dana gargajiya amma babu nasara.

Matar Chori, me suna Faith ta mutu wajan haihuwa. Dalilin hakane Kwange ya aika matarshi dan ta kulawa da Chori jaririn da aka haifa masa.

A nan ne Chori yawa surukar tashi ciki.

Da yake hira da The Sun, Mr Kwange yace ya kadu sosai da jin wannan labari. Bayan da diyarshi dake auren Chori ta mutu a wajan haihuwa, sai yace matarshi Priscilla taje ta yimai rainon jariri, tunda ainahin mahaifiyar Faith itama ta mutu. Yace watanta bakwai kenan a gidan Chori saidai ta waya suke gaisawa.

Yace wanine ya zo ya tsegumta mai cewa ya ga matarshi da ciki amma sai bai yadda ba. Dalilin hakane ya shirya dan ya je yaganewa idonsa. Aikuwa yana zuwa sai yaga matarshi da ciki.

Ya tambayeta yaya akai haka. Sai tace Chorine ya mata ciki kuma ita gaskiya taga ba zata iya zubar dashi ba dan watakila shi kadai ne rabonta lura da cewa ta shafe shekaru 10 babu haihuwa.

Kwange ya kara da cewa da ace lokacin yana sojane to da tabbas babu abinda zai hana ya harbe Chori da matarshi amma yanzu hukuncin da ya yanke shine Priscilla ta bar mai gida sannan shi kuma Chori ya je ya barshi da Duniya.

A nashi bangaren Chori yace bayan da matarshi ta mutu wajan haihuwa yana zaunene tare da kanwarshi dake makaranta kuma ba zata iya hada karatunta da mai rainon jaririn ba. Dan hakane surukarshi ta zo dan ta mai rainon, yace yana zaunene a gida me dakuna 2 dan haka ya barwa surukar tashi da kanwarshi daki 1 shi kuma ya koma amfani da daki 1.

Yace wata rana bai je aiki ba kuma an kwana ruwa, kanwarshi ta tafi makaranta sai ya leka dakin da surukar tashi take dan ya ji yaya suka tashi. Yace sai ya ganta da kayan bacci dan hakane yayi kokarin komawa amma ta ce ya shigo a hakane har ta jashi yayi lallata da ita.

Ya kara da cewa daga nan kuma sai suka ci gaba da yi kullun-kullun a hakane har ta dauki ciki. Yace tace ba zata zubar da cikin ba. Chori yace shi dama Surukinnashi ya kasheshi da yafi mai da abinda yake ji a yanzu.

Saidai yace be ji dadin yanda Surukinnashi ya kwarmatawa Duniya labarinba. Dan abune da ya kamata ace sun warwareshi tsakaninsu.

Priscilla a nata bangaren tace ta jawo hankalin surukinnatane saboda ta gwada ko da gaske tana haihuwa ko kuwa a'a. Tace kuma sai ta samu ciki, ta kara da cewa duk da mijin nata yace ba zata koma mai gida ba, ba zata zubar da cikin ba dan kuwa bata san ko shi kadaine rabonta ba

Ta kara da cewa abinda bata ji dadi ba shine kwarmatawa Duniya labarin da mijinta yayi.

Post a Comment

 
Top