Matashiyarnan 'yar kasar Saudiyya da a shekarar data gabata ta dauki Hankulan Duniya bayan data tsere daga wajan iyalanta data ce suna kuntatawa Rayuwarta da kuma hanata cimma Burin rayuwarta ta kuma yi ridda ta koma kasar Canada da zama, Rahaf Mohammed Al-Qunun ta dauki hankula bayan data saka hoto tsirara-Tsirara.
Ta saka hotonne a shafinta na sada zumunta inda ta hadashi da hotonta lokacin tana Musulma a kasar Saudiyya tana kuma sanye da Niqabi inda ta saka wanda daga ita sai rigar mama da dan kamfai tace da kenan lokacin tana karkashin takura da kuma yanzu data Samu 'yanci.
Saidai wannan hoto data saka ya dauki hankula sosai inda da dama 'yan kasar ta Saudi Arabia suka caccakera akan hakan.
Matashiyar wadda a watan Janairu na shwkarar 2019 ta tsere daga wajan iyalanta lokacin suna ziyartar Kuwait inda ta tafi Bangkok amma aka kwace fasfonta hukumomin kula da shige da fici na kasar suka hanata shiga kasar. Ta yi amfani da wayarta wajan kwarmatawa Duniya halin da take ciki inda ta kulle dakin da take ciki ta ki budewa.
Ta yi ikirarin cewa iyalanta sun ce sai sun kasheta saboda kiyayya. A karshe dai an yi ta kiran kai mata tallafi a kusan Duniya baki daya inda daga karshe ta samu kariyar majalisar Dinkin Duniya kuma ta zabi komawa kasar Canada da zama sannan kuma ta yi ridda inda ta bayyana cewa ita bata yadda akwai Allah bama gaba daya.
Post a Comment