MARYAM Booth ta ƙaryata mawaƙin hip-hop Ibrahim Rufa'i Balarabe, wanda aka fi sani da Deezell, a kan iƙirarin da ya yi a yau cewa ba ya da hannu wajen yaɗuwar bidiyon tsiraicin ta.
bidiyon mai tsawon sakan biyu ya ɓulla a soshiyal midiya inda aka ga fitacciyar jarumar ta Kannywood tsirara zigidir a wani ɗaki.
Wasu kafafen soshiyal midiya sun ambaci Deezell a matsayin wanda ya saki bidiyon don ya tozarta ta bayan soyayyar su ta rushe.
Nan da nan Deezell ya ƙaryata zargin a wata sanarwa da ya bayar a Twitter da Instagram.
To amma Maryam ta ƙaryata shi, ta ce ba shakka shi ne ya ɗauki bidiyon ta a lokacin da ta ke ƙoƙarin saka tufafi.
A cikin sanarwar da ta bayar a karon farko kan wannan badaƙala, wadda ta saka a shafukan ta na soshiyal midiya, Maryam Booth ta ce: "Ina sane da abubuwan da ke wanzuwa yanzu da kuma surutan da ake yi a kafafen yaɗa labarai game da wani bidiyo da aka ce ni ce, aka yaɗa a kafofi da dama na soshiyal midiya, kuma dubban mutane su ka kalla.
"Da farko, na yi niyyar in yi shiru har sai jami'an tsaro sun kammala nazarin su da binciken su.
"Maganar da wani mutum mai suna Ibrahim Ahmad Rufa'i, wanda aka fi sani da sunan Deezell, ya yi, ita ta saka ni tilas in ce wani abu.
"A matsayi na na 'ya mace, 'yar wasa kuma wadda wasu ke kwaikwayo da ita, ba zan bari a shashantar da wannan maganar b
"A gaskiya, ina so in bayyana cewa shi wannan mutum (Ibrahim Ahmad Rufa'i) ya sha yi mani barazanar cewa zai saki bidiyon idan ban ba shi kuɗi ba.
"A matsayi na na 'ya mace, jarumar fim kuma wadda miliyoyin mutane ke koyi da ita, na yi ta ƙoƙarin na kare mutunci na ta kowace hanya da zan iya, amma kawai ba tare da sani na ba sai wannan bidiyo da ya shekara uku da ɗauka ya ɓullo.
"A yanayi irin wannan, tilas mutum ya tsaya ya yi karatun ta-nutsu kafin ya ce komai, amma gaskiya ne cewa Deezell tsohon saurayi na ne wanda kuma shi ne ya ɗauki hoton bidiyo na a lokacin da na ke saka kaya.
"A yanzu ina ta faman tuntuɓar abokan shawara ta don samun hanyar ɗaukar matakin shari'a da ya dace kan dukkan wanda ke da hannu cikin al'amarin sakin wannan bidiyo.
"Ina godiya ga iyaye na da 'yan'uwa na da ƙawaye na da abokai na, da kuma musamman masoya na, saboda yadda su ka nuna tausayawa a gare ne a wannan mawuyacin hali. Na gode maku baki ɗaya.
Maryam Booth
8/2/2020"
Post a Comment