JAMILA Gamdare ta yi fice a finafinan barkwanci tun a zamanin marigayi Rabilu Musa Ɗanlasan (Ibro).

A wancan lokacin babu wata jaruma da ta yi fice a finafinan Ibro bayan rasuwar Hussaina Gombe (Tsigai) kamar ta.

Hakan ne ya sa aka riƙa yi mata laƙabi da Sarauniyar Camama, saboda irin rawar da ta riƙa takawa a finafinan bakwancin, waɗanda ake kira da camama.

To sai dai tun daga rasuwar Ibro sai tauraruwar jarumar ta yi ƙasa, aka daina ganin ta.

Ko da wakilin mujallar Fim ya nemi ganin ta kwanan nan, bai samu nasara ba. Don haka ya yi ƙoƙarin jin ta bakin ta ta waya inda ya tambaye ta ko ta daina harkar fim ne tun bayan rasuwar Ibro?

Sai ta amsa, "To, ina nan a cikin harkar fim, ban bar ta ba kuma ba ni da shirin barin ta domin ita harkar da ita aka san ni a duniya, duk wani abu da na samu albarkacin harkar fim ne, domin yanzu ko aure na yi to darajar fim ta sa aka aure ni. Don haka ina cikin harkar fim har yau har gobe."

Dangane da rashin ganin ta da ba a yi a cikin finafinai kuwa, cewa ta yi,
"To ba a gani na ne, amma lokaci-lokaci ina yin fim.

"Kuma ka san harkar fim ta na da faɗi, ba sai ka na aktin ka ke ɗan fim ba. Don haka ko ban yi aktin ba ina yin wasu harkoki a cikin masana'antar, kamar waƙa da ɗaukar nauyin fim da sauran su.

"Don haka ina cikin harkar fim ban fita ba, domin ita harkar fim kamar kabari ce, idan an shiga ba a fita, kawai sai dai fatan cikawa da imani!"

Mujallar Fim ta tambayi Jamila Gamdare yadda ta ke ganin harkar fim a yanzu.

Sai ta ce, "To idan ma akwai dalilin da zan ce shi ya sa ba a gani na, sai dai in ce shi ne yanayin yadda harkar ta ke a yanzu, domin yanayin da masana'antar ta samu kan ta a ciki shi ne ya ɓoye kowa, don haka mutane su na bin wasu hanyoyi wanda za su rufa wa kan su asiri, amma dai harkar fim ɗin dai ita ce ta zame mana jagora, duk inda mu ka je to cikin ta za mu dawo."

Daga ƙarshe jarumar ta yi fatan harkar fim za ta dawo cikin hayyacin ta. A cewar ta, "Halin da harkar fim ta ke ciki a yanzu, sai dai addu'ar Allah ya kawo mana mafita."

Post a Comment

 
Top