Duk da cewa an fi yin kaciyar mata a wasu kasashen Afirka da gabas ta tsakiya 30, a wasu kasashen Asiya da Latin Amurka ma ana yi wa mata kaciya.
Haka ma tsakanin al'ummomi baki mazauna yammacin turai.
Majalisar Dinkin Duniya ta ware ranar shida ga watan Fabrairu na kowacce shekara a matsayin ranar wayar da kai da kuma yaki don kawo karshen yi wa mata kaciya.
Matan da aka yi wa kaciyar na samun rauni ko tabin hankali daga baya, kamar yadda Bishara Sheikh Hamo daga yankin Borana a lardin Isiolo na kasar Kenya ta bayyana.
"An yi mini kaciyar mata ina 'yar karama,'' in ji ta. "A lokacin kakata ta fada mani cewa abu ne da ake yi wa kowace 'ya mace domin yana tsarkake su."
Sai dai ba a fada wa Bishara cewa kaciyar na iya haifar mata da rikicewar al'ada da matsalar mafitsara da yawan kamuwa da cutuka na tsawon rayuwa ba.
Haka kuma ba a fada mata cewa nan gaba ba za ta iya haihuwa ba sai an yi mata tiyata.
Yanzu tana aikin wayar da kai game da illar yi wa mata kaciya.
Mece ce kaciyar mata?
Kaciyar mata ita ce yankewa ko cire wani bangare da ke wajen al'aurar mata.
Ta kunshi yanke dumbaru, kuma Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana ta a matsayain "duk wani abin da ke haifar da rauni ga al'aurar mace ta wata hanya ba ta likitanci ba".
Kaciyar mata hadari ce ga mata kuma tana yin illa ga yadda mata ke daukar kawunansu, in ji wata mawallafiya a intanet, Omnia Ibrahim.
Tana mayar da mace kakkausa kamar kankara. Ba za ki ji kauna a ranki ba, ba za ki ji sha'awa ba," in ji ta.
Omnia ta ce ta yi fama da matsalolin da ke da alaka da kaciyar mata a tsawon rayuwarta a matsayin baliga.
Ta ce al'ummar da ta taso a ciki sun cusa mata tunanin cewa "jiki tamkar yin jima'i ne kuma yin jima'i sabo ne. Kula da jikina ya zama tamkar wani alkaba'i ne a ganinsu."
"Na kan tambayi kai na: Shin ba na son yin jima'i ne saboda ban damu da shi ba ko kuma dai saboda an sa in rika jin tsoro ne?"
Bishara ta shaida wa BBC cewa an yi mata kaciya ne tare da wasu yara mata hudu a Kenya.
"An rufe mani ido sannan aka daure hannayena ta baya. Aka bude kafafuna sannan aka fito da bakin al'aurata."
"Bayan wasu mintoci, sai na ji radadi. Na yi kururuwa amma ba mai ji na. Na yi kokarin fincike kafata, amma sai na ji wani karfe ya rirrike kafafuna."
Ta ce akwai ban "takaici. Yana daga cikin aikin fida mafi tsanani da hadari ga lafiya. Sun yi mani amfani da askar da aka yi wa sauran 'yan matan amfani da ita".
Babu wani abin kashe radadin sai wani ganye.
"Akwai wani rami da kasa aka sa ganye a ciki. Sun daure kafauna kamar wata akuya sannan suka shafe mani jiki da ganyen.
"Daga nan sai suka ce a kawo yarinya ta gaba, sannan suka dauki yarinya ta gaba da za a yi wa kaciyar...."
Duk da cewa kasashe da yawa sun haramta yi wa mata kaciya, ana yawan yin ta a wasu kasashen Afirka da Asiya da Gabas ta tsakiya - da wasu sassan duniya a al'ummomin da ake yawan yin kaciyar matan.
Kaciyar mata iri hudu ce:
Nau'i Na Farko: Cire dumbaru gaba daya tare da fatar da ke kwaye da ita.
Nau'i Na Biyu: Cire dumbaru ko bangarensa tare da cire fatar da ke zagaye da farjin mace ta ciki.
Nau'i Na Uku: Yankewa tare da sauya wa fatar farji yanayi. Ya hada da dinki ta yadda ake barin wata karamar kofa.
Wannan nau'i na da tsananin zafi da tashin hankali tare da haifar da cuta ga fata: ana toshe kofar farji da mafitsara sannan a bar wa matan wata 'yan kofa domin yin fitsari da fitar jinin al'ada.
Wani lokaci kofar kan yi kadan har sai an kara girmanta domin a iya saduwa da macen ko ta iya haihuwa - wanda yakan haifar da matsala ga jariri da mahaifiyarsa.
Nau'i naHudu: Ya kunshi sauran nau'ikan da aka ambata a baya da suka hada da hudawa da yankawa da gogewa ko kona dumbaru da sashen al'aurar mace.
Me ya sa ake yi?
An fi ambaton al'ada da addini da mummunar fahimta fiye da lafiya a matsayin hujjar yi wa mata kaciya da sunan hanyar kare budurcinsu domin su samu auruwa da kuma kara masu ni'ima wurin saduwar aure.
A wasu wuraren kaciyar mata wata al'ada ce da ake yi yayin shiga matakin balaga da kuma a matsayin sharadin aure.
Duk da yake babu wata fa'ida a likitance da kaciyar mata ke da ita, al'ummomin da ke yin ta sun yi amannar cewa akwai bukatar yi wa mata ita, suna kuma kallon matan da ba a yi masu ba tamakar marasa lafiya ko marasa tsarki ko kamala.
Galibin matan ba da son ransu ake masu kaciya ba. Kwararru a fannin lafiya a duniya na daukar kaciyar mata a matsayin cin zarafi da tauye hakkin mata.
Haka kuma ana daukar ta a matsayin cin zarafin kananan yara a duk sadda aka yi wa yara ita.
A ina ake yin ta?
Yawancin matan da Asusun Yara na MDD UNICEF da Hukumar Lafiya ta Duniya WHO suka tambaya sun ce al'ummomin da suka fito na ganin yin magana game da kaciyar mata wani alkaba'i ne, shi yasa ake kiyasin al'kaluman da aka bayar.
Wani lokaci matan ba sa yin magana a fili game da ita saboda gudun suka daga jama'a.
A wasu lokutan kuma - a wuraren da aka haramta yi wa mata kaciya - tsoron gurfanar da iyalai ko al'ummar a gaban shari'a ne ke hanawa.
Shirin samar da alkaluman a kan mata ta Woman Stats Project ce ta samar da jadawalin da ke sama ta hanyar hada bayanan da aka samu game da batun da wadanda ta samu daga MDD da UNICEF.
MDD ta yi kiyasin cewa ko da yake an fi yi wa mata kaciya a kasa 30 a nahiyar Afirka, a yankin gabas ta tsaikiya da wasu kasashen Asiya da Latin ma ana yi.
Ana kuma yi a al'ummomin baki mazauna yammacin Turai da Arewacin Amurka da Australi da da kuma New Zealand.
Rahoton binciken da UNICEF ta gudanar a kasashen Afirka 29 da gabas ta tsakiya ya nuna cewa ana yawan yin kaciyar mata, duk da cewa 24 daga cikin kasashen sun yi dokokin haramta yin ta.
A kasashe irin Birtaniya inda aka haramta kaciyar mata, wata kwararriya kuma lauya Charlotte Proudman ta ce ana yawan yin ta ga kananan yara, kuma yana da matukar wuyar a gano domin yaran ba su fara zuwa makaranta ba ko kuma ba su da wayon da za su iya kai rahoto.
A shekarar 2019, wata uwa - 'yar asalin Uganda - ta zama mutum na farko da aka samu da laifin yin kaciyar mata ga 'yarta mai shekara uku.
©HausaLoaded
Post a Comment