Maniyi ruwa ne dake fitowa daga azzakarin namiji a lokacin da yake saduwa da matar sa ko kuma lokacin da jinsin mace da na miji ke tarayya da juna.

A lokutta da dama mutane musamman mata kan tambayi likitoci ko akwai hadari ga lafiyar mace idan tana hadiye maniyin mijin ta a lokacin da suke saduwa?

Jen Anderson dake kasar Amurka ta yi kokarin bayyana amfani da illar dake tattare da hadiye maniyin namiji wanda aka wallafa a shafin ‘Heathline’ dake yanar gizo.

1. Hadiye maniyin namiji baya cutar da kiwon lafiyar mace domin maniyi na dauke da sinadarin ‘Glucose, sodium, citrate, zinc, chloride, calcium,lactic acid, magnesium, potassium wanda ke taimakawa wajen inganta kiwon lafiyar mace.

Sai dai bincike ya nuna cewa mace za ta fara ganin amfanin wadannan sinadarori a jikinta idan tana yawan kwankwadar maniyin.

2. Hadiye maniyi na kare mace mai ciki daga kamuwa da cutar hawan jini.

Bincike ya nuna cewa maniyi na dauke da sinadarin ‘Endorphins, estrone, prolactin, oxytocin,throtropin da serotonin wanda ke hana mace mai ciki kamuwa da hawan jini.

3. Hadiye maniyi na kawar da damuwa ko kuma yawan fushi ga mata da maza gabada saboda wadannan sinadari da yake dauke da su

4. Ana iya kamuwa da cututtuka na sanyi dake kama al’auran mutum.
Bincike ya nuna cewa mace za ta iya kamuwa da cututtuka irin ta sanyi kamar su ‘Gonorrhea,Chlamydia,syphilis da sauran su sannan kuma da kanjamau idan har namijin na dauke da wannan cututtuka

5. Yana kara kyan fatar mace musamman wajen hana kuraje a fuska.

6. Hadiye maniyi na sa barci mai nauyi
Hakan na yiwuwa ne a dalilin dauke da sinadarin ‘Melatonin’ wanda ke taimaka wa wajen barci.

7. Yana kara kiba a jiki domin akwai kitse daban-daban har kashi biyar zuwa bakwai dake sa kiba a jiki.

8. Maniyyi kan dan yi wari, sai dai likitan ta bayana cewa warin maniyi ya danganta da irin abinci da tsaftan namiji. Wani yakan yi dandanon siga-siga, wani kuma gishiri-gishiri.
PThausa.

Post a Comment

 
Top