Wata mata me shekaru 25 ta guntulewa wani Mutum dake shirin Angwancewa da Masoyiyarshi kwannan mazakutarshi bayan da yayi yunkurin yi mata fyade.

Lamarin ya farune a yankin Funjab dake kasar Pakistan inda mutumin ya sami matar a gida yayi yunkurin afka mata.

Data lura da haka sai ta tafi dakin dafa Abinci ta wawuri wuka, nan kuwa bata yi wata-wata ta guntule masa abinsa.

Kamfanin Dillancin Labaraj kasar DPA ya ruwaito 'yansanda na cewa an garzaya da matashin me shekaru 28 zuwa Asibiti inda aka basgi kulawar data kumata kuma tuni aka fara binciken lamarin.

Saidai an gano cewa Matar da mutum dama sun san juna tun tuni.

Mata da dama ne akewa fyade a kasar ta Pakistan duk shekara ba tare sa hukunta masu aikata laifukan ba.

Post a Comment

 
Top