...layukan waya 3 kacal kowanne dan Nijeriya zai iya mallaka

Daga Comr Abba Sani Pantami

Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na dijital, Dr. Isa Ali-Pantami ya umarci Hukumar Sadarwa ta Kasa, NCC, da ta tabbatar da cewa Lambar Shaida ta Kasa ta NIN, ta zama tilas ga ‘yan Najeriya yayin yin rijistar sabbin layukan SIM, 'yan kasashen waje, za su dinga amfani da Visa, ko fasfo din su domin yi musu ragista Kamar yadda Daily Nigeria ta fitar.

Ministan ya ba da wannan umarnin ne a ranar Laraba a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun Mataimakin sa, Dakta Femi Adeluyi, inda ya umarci Hukumar NCC da ta sake fasalin Manufofin yin rijistar katin SIM din.

Sanarwar ta kuma lura cewa sake fasalin manufar ta dogara ne akan martanin da aka karba daga hukumomin tsaro, sakamakon nasarar sake fasalin katinan da aka yiwa rajistar a watan Satumbar 2019 da kuma toshe wadanda suka kasa saka layukansu a wayoyin su.

Ministan ya kuma umarci hukumar da ta tabbatar da cewa, layukan 'yan Nigeria, da zasu mallaka kada ya wuce akalla guda ukku.

A cewarsa, za'a sake sabunta rajista da nomban NIN kafin 1 ga Disamba 2020.

Ga sauran tsare tsaren da ministan ya bayar, kamar haka;

 A tabbatar da cewa amitattun dillalai ne zasu rika siyar da layi, haka zalika kamfani ne kadai zai iya yi wa layi rijista.

Layukan waya 3 kacal kowanne dan Najeriya zai iya mallaka.

 A tabbatar da babu layin da zai yi aiki face sai da rijista.

A tabbatar da cewa kowa zai iya ganin bayanan da aka shigar wajen yin rijista kai tsaye ta waya.

Dole kamfanonin sadarwa su yaki ta’addanin ko barnar yanar gizo.

A tabbatar da rufe dukkanin wani ds aka samu da amfani wajen aikata miyagun laifuka.

Sanarwar ta "Tabbatar da cewa zasu Tabbatar da  katunan SIM wadanda aka yi amfani da su wajen aikata manyan laifuka an lalata su har abada."

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top