Babu Soyayya Tsakanina Da Mawaki Akon – Inji Rahma Sadau

Babu Soyayya Tsakanina Da Mawaki Akon – Inji Rahma Sadau.

Jarumar fim din hausa tayi magana akan cewa ita babu soyayya tsakaninta da mawakin amurka Aliane Damala Bouga, wanda akafi sanin sa da Akon.

Rahma Sadau ta fadi haka ne a gidan talabijin Arewa 24 a shirin Kundin Kannywood wanda Aminu Sharif Momoh shine yake gabatar da shirin a ranar talata.

“Banyi taba tunanin zan hadu Akon ido da ido ba. Nasan wakokin sa dadewa kafin yanzu domin shi shahararen mawakine .
Lokacin dana amshi gayyatar shi nayi mamaki matuka naga wannan babbar damace da bazan iya wasa da ita ba” Inji Rahma Sadau

Lokacin da aka tambaye ta akan cewa yana son canza mata addini Rahma Sadau ta karya wannan jita-jitar tace wanda suke yada jita-jitar basu san Akon bane sabida shi mutum ne wanda yake aikata aiki irin na musulmai .

Tace ya gayyace ma suje umrah tare amma tace masa aa sabida tasan mutanen mu yazo zasu fara hada nasu labarin.

Rahma Sadau tayi magana akan sabon fim dinta wanda zai fito Mai taken “Mati A Zazzau”

The post Babu Soyayya Tsakanina Da Mawaki Akon – Inji Rahma Sadau appeared first on ArewaFresh.com™.


©Arewafresh

Post a Comment

 
Top