Rahama Sadau, Yakubu Mohammed za su fito a wani sabon kayataccen Fim na turanci

Rahama Sadau, Yakubu Mohammed za su fito a wani sabon kayataccen Fim na turanci

Shahararriyar tauraruwar fina finan Kannywood, Rahama Sadau za ta goga kafada da kafada da wasu fitattun yan fim don turanci na Najeriya, watau Nollywood a wani sabon Fim da zasu fito a ciki mai suna MTV Sugar Naija 4.

Rahoton jaridar Daily Trust ta bayyana cewa daga cikin wadanda zasu fito cikin wannan shiri akwai Richard Mofe Damijo-RMD, Funsho Adeolu, Funlola Raimi, Ruby Akubueze, Osas Ighodaro, Omawunmi Dada, Yakubu Muhammad, Belinda Yanga da sauransu.

Kamfanin dake shirya shirin, MTV Staying Alive sun bayyana cewa wannan sabon shirin zai kunshi tsofaffi da sabbin yan Fim, daga ciki har da wasu sabbin yan Fim masu tasowa wanda suka doke sama da mutum 1,000 da suka halarci tantancewa.

Guda daga cikin yan Fim din, Timini Egbuson ya bayyana farin cikinsa da sake samun daman fitowa a shirin kashi na 4, inda yace ya samu karin ilimi sosai game da harkar Fim tun farkon fara kashi na 1, sa’anann ya tabbatar da cewa masoya fim din ma sun karu.

Da yake kara haske kan makasudin shirya Fim din, shugaban MTV gidauniyar Staying Alive, Georgia Arnold ya bayyana cewa: “ Akwai labarai da dama da sabon shirin zai kunsa, tun daga takaita haihuwa, tsara iyali, rikicin jinsi, da sauran labarai da suka shafi yan kallo.

“Haka zalika baya ga cewa mutanen da muka zabo don yin wannan Fim kwararru ne, mutane ne dake isar da sakonmu zuwa ga jama’a da dama, tare da yin tasiri a kan matasan Najeriya dayawa.” I nji shi.

Daga karshe wannan Fim zai samu tallafi daga kwamitin kididdigar jama’a na majalisar dinkin duniya don isar da sakon ilimin jima’I a tsakanin matasa, daukan ciki na kananan yara, da kuma tsara haihuwa ga kananan mata da aka yi ma aure.

Ga kadan daban guntun videon wani shiri da sunka fito

Download Now

The post Rahama Sadau, Yakubu Mohammed za su fito a wani sabon kayataccen Fim na turanci appeared first on ArewaFresh.com™.


©Arewafresh

Post a Comment

 
Top