Tsohon gwamnan jihar Zanfara, Abdulaziz Yari Abubakar yace ba a samu wani abu na laifi ba a lokacin da hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta kai samame gidansa da ke Talata Mafara a ranar Lahadin da ya gabata.

Hadimin gwamnan, Malam Ibrahim Dosara, ya bayyana a wani jawabi da ya saki a jiya cewa:

An ja hankalina akan wani labari da ake yawo cewa wassu jami’an EFCC sun shiga gidan tsohon gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari Abubakar a Talata Mafara sannan cewa sun tafi da wasu kaddarori.

“A wannan yanayin ne naga ya kamata in yi tsokaci akan al’amuran zuwa ga jama’a.

“Gaskiya ne cewa wasu jami’an hukumar EFCC a ranar Lahadi, 3 ga watan Agusta, 2019 sun shiga gidan tsahon gwamnan a Talata Marafa.

“Ko da yake, ba a gane dalilin kai ziyaran nasu gidan ba, tsohon gwamnan ya bada umurnin cewa a bude dukkan dakunan da ofisoshi da ke gidan don gudanar da binciken. Bayan bincike na sa’o’i biyar, jami’an sun tafi ba tare da daukan komai ba.



“Duk da haka, ina bayyana ma al’umma cewa ba a samu komai na laifi ba a gidan, sannan ba a kuma tafi da komai ba.

“Saboda haka, mun bar EFCC su gudanar da aikinsu kafin cigaba da gabatar da duk wani bayani kan lamarin.”

® Legit

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top