Jami’an hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC sun kai wani samame gidan tsohon gwamnan jahar Zamfara, Abdul Aziz Yari, dake garin Talatar Mafara domin gudanar da bincike.

Legit.ng ta ruwaito shaidun gani da ido sun bayyana cewa jami’an hukumar da yawansu ya kai mutum 20 sun dira gidan tsohon gwamnan ne da misalin karfe 6 na yammcin Lahadi, inda suka kai har zuwa karfe 11 na dare suna bincike.


Sai dai har zuwa lokacin tattara wannan rahoto babu tabbacin ko jami’an sun bankado wasu abubuwa a gidan, amma majiyoyi sun tabbatar da cewa daga gwamnan har iyalansa babu wanda ke cikin wannan gida a lokacin da EFCC suka isa.

Haka zalika an jiyo mazauna garin Talatar Mafara da suka yi cincirindo a kofar gidan suna kabarkarin ‘Allahu Akbar’ yayin da jami’an hukumar EFCC suka gudanar da binciken nasu, da nufin nuna adawarsu da abinda EFCC ke yi ma tsohon gwamnan.




A makon data gabata ne dai dan takarar gwamnan jahar Zamfara a inuwar jam’iyyar APGA, Sani Shinkafi ya nemi wata kotu ta tilasta ma hukumar EFCC gudanar da cikakken bincike a kan mulkin Abdul Aziz Yari.

Shinkafi yana zargin Abdul Aziz Yari da wawuran naira biliyan 251 daga asusun gwamnatin jahar Zamafara, sa’annan ya tana tuhumarsa a kan barin ayyuka da bai kammala ba da suka tasan ma naira biliyan 151.190.

Sai dai har zuwa lokacin tattara wannan rahoto, ba’a ji amon hukumar EFCC game da wannan samame ba.


©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top