Sunan Fim:  Wakili

Kamfanin da ya shirya:  Garkuwa Empire da Dorayi Flims & Distributions LTD



Shiryawa:  Falalu A. Dorayi

Tsarawa:  Nazir Adam


Umarni:             Falalu A. Dorayi

Shekara:  2019

Mai sharhi: Ibrahim Babangida Surajo



’Yan wasa: Ali Nuhu, Falalu Dorayi, Aminu Momoh, Garzali Miko, Umar Gombe, Rabiu Daushe, Sulaiman Bosho, Tijjani Asase, Hadiza Gabon, Aisha Tsamiya, Hannatu Bashir da sauransu.



Fim din Wakili labari ne kan wata mummunar al’ada da ta addabi al’umma da aka shirya cikin barkwanci da nishadi. Fim din ya yi nuni a kan mugun halin gurbatattun shugabanni, inda suke amfani da matsayinsu suna aikata laifuffuka da dama.

Yadda ake cika silima wajen kallon fim din a duk inda aka nuna shi ya nuna yadda fim din ya samu kyakkyawan aiki da tsari. Domin  wani basarake ya yaba da fim din, duk da cewa an nuna yadda wadansu sarakuna suke bata sarauta.

Da aka nuna fim din a gidan silima na Film House da ke Kano, sai da tikitin shiga kallon ya kare baki daya. Washegari ma aka sake tururuwa domin zuwa sake kallon fim din.

Manyan jigogin fim din su ne sarauta cikin barkwanci da al’adar auren kisan-wuta.

A cikin shirin, Sulaiman Bosho (Wakili) shi ne ya fito a matsayin basarake, wato Dagaci, wanda ake kiransa Wakili a cikin shirin, sannan babban Wazirinsa shi ne Falalu Dorayi wanda yake take masa baya da shirya masa yadda zai yi duk abin da yake so.

Daga cikin ayyukan da Wazirinsa (Falalu Dorayi) yake taimaka masa wajen aikatawa, akwai nemo yadda za a shawo kan mace idan ya ganta yana so.

Akwai inda Wakili ya ga Hannatu Bashir yana so, kuma yana so yayi mata Ingilishi amma bai iya ba, sai Wazirinsa (Falalu) ya rubuta maganar da zai yi a allo ya tsaya a bayan Hannatu ya daga allon, shi kuma Wakili yana karantawa.

Da abu ya kai abu, sai Wazirin ya dauki Wakili ya kai shi wajen wanda yake koyar da soyayya na zamani (Umar Gombe) domin ya koya masa yadda zai rika shawo kan mata ’yan zamani cikin sauki.

Nan take malamin soyayyar ya fada wa Wakili cewa babin farko wajen sace zuciyar mace shi ne sakin fuska, Wakili ya ce, “Basarake ba ya son raini.” Sannan aka ce dole ya saki fuska sannan ya kashe mata ido, inda shi ma waziri ya ce, “Ai kashe ido iskanci ne.”

A dayan bangaren kuma, akwai Garzali Miko (Tela) wanda Wakili ya yi amfani da shi wajen auren kisan-wuta, domin Hadiza Gabon (’Yar Hidimar Kasa NYSC) ta shaida wa Wakili cewa aurenta ya mutu kuma tana son komawa gidan mijinta. Garzali ya amince ya aure ta, amma kuma ba ta bin dokokinsa, inda har yake ce mata yawan fita da take yi tana yi a wuta, nan take ta ce masa, “Ai kai ne babban dan wuta, ba ka san auren kisan-wuta ka yi ba?”

A wani bangaren, Ali Nuhu shi ne ya fito a matsayin Alkali mai son naman zabi. Da Wakili ya je wajensa da zabi, sai Alkali ya tambaye shi, sai ya ce, “Ai na san ba ka karbar cin hanci. Da kai da cin hanci kamar Gabas da Yamma ne.” Sai Ali Nuhu ya ce ya ce masa ai ya fi son ya daure na kusa da shi domin ya nuna darasi a kan sauran.

Majiyarmu ta samu daga aminiyahausa,Da sauran fuskoki da suka fito da jigon fim din. Fim din ya tsaru matuka, domin an yi amfani da gwanintar harshe wajen isar da sako cikin sauki da nishadi domin ba kowa ba ne yake iya isar da sako cikin barkwanci kuma sakon ya isa, musamman inda aka yi amfani da kirkira.  Misali, da karshen Wakili ya fara zuwa, inda ya shiga tarkon Tijjani Asase, nan take Wakili da Wazirinsa suka fara waka suna cewa, “Ye! Mai Girma Yesu na tuna da laifina!”

Haka kuma a inda Wakili yake son ya nuna cewa yana da masaniya a kan asalin NYSC, sai ya ce, “Asalin NYSC wani Bature ne mai suna Albaro Morata ya kirkiro shi.”

Da yake bayani kan dalilinsa na shirya fim din, Darakta Falalu Dorayi ya ce an shirya fim din ne domin a nusar da mutane halayen wadansu masu rike da mukamai musamman masarautun gargajiya, wadanda suke amfani da su ta hanyar da ba ta dace ba musamman wajen aikata miyagun halaye a boye domin suna ganin sun shiga cikin inuwar mutuncin sarautar da suke da ita.

Fadakarwa


Fim din ya bayyana daya daga cikin manyan matsalolin da suka addabi al’umma. Wato amfani da karfin mulki.

Daga cikin abubuwa da za a koya a cikin fim din akwai: Labarin ya nuna cewa sarakuna suna da matukar tasiri a cikin al’umma, musamman Hausawa, don haka ya kamata su rika yin adalci da nuna natsuwa. Kamar yadda Hadiza Gabon ta kawo kukan cewa aurenta ya mutu kuma tana so ta koma gidan mijinta, inda Wakili ya nuna cewa idan auren kisan-wuta take so, shi ma zai iya kashe mata wutar tunda yana da mulki.

Fim din kuma ya nuna cewa komai nisan jifa kasa zai dawo da sauran darussa da za a koya masu dimbin yawa a cikin shirin.

Duk wanda ya kalli fim din, zai tabatar da cewa fim din ya nishadantar da masu kallo, wadanda ba su kalla ba, kuma sai hanzarta su nemi fim din domin su nishadantu. Za a haska fim din a otel din Teejay Palace da ke Zariya a ranakun Sallah.

Abubuwan burgewa

Wanda ya tsara fim din ya yi kokari matuka wajen tsara shirin, kuma wanda ya jagoranci ci gaban shirin domin labarin ya tafi ba tare da yankewa ba.

Daraktan fim din shi ma ya yi kokari wajen jagorantar fim din, sannan wadanda suka dauki nauyin fim din sun yi kokari wajen amfani da manyan kyamarori don daukar shirin.

Sannan an yi amfani da wakokin gada irin na al’adar Bahaushe masu fadakarwa.

Wani abin burgewa da fim din shi ne yadda aka yi amfani da kyamarori manya na zamani musamman lura da yadda sauti ya fito radau, hoto ya fito garau, sannan kowane dan wasa ya yi kokari wajen nuna kwazo. Sannan uwa uba, Daraktan fim din Falalu A. Dorayi wanda yake shirya fina-finan barkwanci da suke yin fice irin su, Namamajo da Andamali da sauransu ya yi matukar nuna bajinta wajen isar da sako mai girma cikin nishadi da barkwanci.

Sai dai kamar yadda ake cewa, mutum tara yake bai cika goma, wani abin lura shi ne a matsayin Bahaushe da aka san shi da kunya, kuma aka san al’adar Hausa da girmama masarautu wadanda ko suna aikata laifi ba a cika son yin magana a kai ba, har za ka ji ana cewa ba za a ji mutuwar sarki a bakina ba, don haka bai kamata a ce soja ya kama Wakili da duka ba har ya kai yana buga shi a kasa. Da kuma sauran kura-kurai da ba za a rasa ba.

A karshe ina fata wannan sharhin zai amfanar, Allah Ya taimake mu, amin.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top