Kasar Amurka ta karrama fitaccen jarumin fina-finan Hausa na kungiyar Kannywood Ali Nuhu

- Kasar ta karramashi karkashin ofishinta na jakadanci dake babban birnin tarayya Abuja a ranar Litinin dinnan da ta gabata

- Kasar ta ce Ali Nuhu ya taimaka a wurare da dama wajen kawo cigaba a kasar nan da samawa matasa aikin yi

Kasar Amurka karkashin ofishinta na jakadanci dake babban birnin tarayya Abuja ta karrama fitaccen jarumin fina-finan Hausan nan na kungiyar Kannywood, Ali Nuhu.

Kasar ta karrama fitaccen jarumin ne a wata sanarwa da ta fitar wacce ta wallafa a shafinta na sada zumunta na Facebook a ranar Litinin dinnan da ta gabata.

Ofishin ya bayyana cewa kasar ta karrama jarumin ne saboda irin nasarorin da yake samu wajen yiwa kasar Najeriya hidima da kuma taimakawa matasan Najeriya da ayyukan yi.


Fitaccen jarumin wanda aka fi sani da Sarki Ali, yana daya daga cikin ginshiki na wannan masana'anta ta Kannywood, ya bayar da umarni a fina-finai kala, sannan ya kuma shirya fina-finai masu yawan gaske karkashin kamfaninsa na hada fina-finai mai suna FKD.

Kasar ta ce banda fina-finan da jarumin ya shirya, Ali Nuhu ya kasance mutumin da ya shigar da matasa masu dumbin yawa cikin masana'antar Kannywood.

Sannan kuma shine yayi fadi tashi wajen kulla alaka tsakanin masana'antar Kannywood da ta Nollywood. Kuma ya hada kai da wasu mutane wajen samar da fina-finai masu ma'ana a masana'antar.

Amurka ta bayyana cewa tana sane da irin lambobin yabon da Ali Nuhu ya lashe a Najeriya da kuma kasashen duniya baki daya.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top