Hukumomin Saudiyya sun zabi Malam Dakta Magaji Falalu Zarewa ne don sauke wannan nauyi, tare da gabatar da karatuttuka a wannan Masallaci mai albarka dake samun dimbin baki yan Najeriya Hausawa da kuma masu jin yaren Hausa.
Legit.ng ta ruwaito hukumomin kasar Saudiya sun tsayar da lokacin bayan sallar Magariba da sallar Isha’I na kullum don ya kasance lokacin da za’a Malam Zarewa zai dinga gudanar da wannan karatu.
A wani labarin kuma, hukumar alhazan Najeriya ta kammala jigilar mahajjatan Najeriya da suka kai 44,450 zuwa kasar Saudiyya daga jahohin 36 da babban birnin tarayya Abuja domin gudanar da aikin Hajji. Sai dai wannan adadi bai hada har da mahajjatan jirgin yawo ba.
Gwamnatin kasar Saudiyya ta baiwa gwamnatin Najeriya kujeru 95,000, inda gwamnatocin jahohi suka samu kujeru 65,000 yayin da kamfanonin jiragen yawo suka samu kujeru 30,000.
A ranar Litinin, 5 ga watan Agusta ne jirgin karshe ya tashi daga babban birnin tarayya Abuja dauke da maniyyata 301 da jami’an hukumar alhazai guda 19, inda ya tashi da misalin karfe 8:53 na dare.
Jirgin na 93 mallakin kamfanin Flynasa mai lamba XY5821 ya kwashi ragowar mahajjatan jahohin Abuja, Sakkwato, Abia, Enugu, Ebonyi, Delta, Cross Rivers, Delta, Zamfara, Kaduna da Anambra.
Zuwa ranar Litinin an samu alhazai 1,687,226 daga dukkanin sassan duniya sun isa kasar Saudiyya ta ruwa, ta jirgin sama da kuma ta kasa don gudanar da aikin Hajji a kasar Saudiyya.
® Legit
©HausaLoaded
Post a Comment