Kafin mu shiga cikin bayani ya kamata mu san shin wace ce bazawar, budurwa da kuma wacce ta girmi mijinta.
Bazawara dai ita ce matar auren da suka rabu da mijinta sanadiyyar mutuwa ko kuma rabuwa. Budurwa kuma ita ce wacce ba ta taba yin aure ba. Sannan ita kuma matar da ta girmi mijinta ita ce, wacce ta fi mijinta shekaru, wato ta riga shi zuwa duniya.
Mafiya yawan samari ba sa son auren bazawara, amma masana sun yi nuni da cewa, akwai fa’idoji mai yawa game da auren bazawara ko kuma wacce ta girmeka. Ga kadan daga cikin fa’idojin.
Yana daga wasu fa’idoji da namiji zai samu in ya auri matar da ta girme shi ko bazawara kamar haka.
-Na farko zai samu ladan sunna, idan ka yi domin yin koyi da fiyayyen halitta.
– Auren mace wacce ta fi ka shekaru akwai yuyuwar samun ingantacciyar rayuwar aure matukar akwai soyayya sakamakon cewa, ita ta zauna da wasu mazan ta san rayuwar aure, ta san mai namiji yake so ta san abin da baya so, ta sami kwarewar iya kwanciya da miji, sabo da haka da zarar ka auri irin wannan kuma akwai so da kauna da tarbiyya, to ba ma auren da ya fi shi dadi, sakamakon ta sami karewa koda ba ta taba aure ba a bayan shekarun da ta yi a rayuwarta, zai sa ta ga abubuwa kalakala a rayuwarta wadanda za su zama mata darasi a zamantakewar aure nan gaba.
-Hakika bazawara ta fi budurwa sanin makamar aiki a zamantakewar aure musamman ma in ta sami saurayi wato wanda ta girma, musamman ma a ce akwai soyayya.
-Bazawara tana da hakurin zamantakewa fiye da budurwa, domin ita budurwa ta kware wajen yaudara.
Bazawara ko wacce ta fi ka shekaru ta san halayen iyayen miji da yadda ake zama da su sabanin budurwa.
-Ayyukan gida, kula dagi, gyaran daki, iya girki da tsaftace shi, kula da yara da shauran su dukkan su zawarawa ta fi budarwa kwarewa a kai.
-Dadin kalamai, kisisina, iya rarrashin miji, rashin katobara yayin zance, dadin fira dukka zawarawa ta fi kwarance fiye da budurwa.
-Rashin almabazzaranci da dukiyar maigida, kamar bata abinci, wasa da shi da sauransu, bazawara ta fi saukin a kan budurwa.
©HausaLoaded
Post a Comment