Yaya a wurin Sheik Ibrahim El-zakzaky Shugaban kungiyar Islamic Movement of Nigeria (IMN) wadda aka fi sani da Shi’a, Sheikh Muhammad Sani Yakub ya yi fashin baki a kan haramta ayyukan shi’a inda ya ke cewa hakan ya yi daidai.
Sheikh Muhammad Sani wanda yake babban wa ga Ibrahim El-Zakzaky shi ne Shugaban Kungiyar Izala ta Zariya. Kuma ya furta wannan maganar tasa ne a wata hira ta musamman da ya yi da manema labarai a Zariya, kamar yadda majiyarmu ta Legit Hausa ta rawaito
A cewarsa ba haramta ayyukan shi’an kawai ya kamata gwamnati tayi ba, gaba daya ya kamata a ce an kori kungiyar daga Najeriya.
Haka zalika, ya kara da cewa wannan kungiya ta shi’a bata da wani bambanci da kungiyar Boko haram, inda ya ce kaninsa El-Zakzaky bai da bambanci da Shekau.
Sheikh Muhammad Sani ya ce: “ Kamar yadda kuka sa ni dai El-Zakzaky dan-uwana ne na jini, mahaifinmu daya da shi. A lokacin da muka taso bani da abokin da ya wuce shi kafin ya fara shi’a kenan. Komai namu tare muke yi hatta makaranta ma daya muke zuwa ta islamiya.
“ Mun yita ja masa kunne a kan wannan bakar akida amma ya ki ji. A gani na tun da dadewa ya kamata a ce gwamnati ta sallami al’amuran wannan kungiyar saboda babu wani abu mai kyau a tare da kungiyar shi’a.
“ Wai shin in tambayeku mana, a duk fadin duniyar nan ina kuka taba ganin an rufewa Hafsun sojoji hanya?
Amma a kasar nan ‘yan shi’a sunyi hakan, sai yanzu gwamnati ta ga cewa ya kamata ta haramta ayyukansu. Babu wani laifi da gwamnati tayi abinda akayi ya dace dari bisa dari.” Inji yayan Zakzaky.
©HausaLoaded
Post a Comment